Masu kula da kan iyaka a Roma da ke Texas na yi wa ƴan ci rani rijista, bayan da suka tsallake kogin Rio Grande daga Mexico. Ana ci gaba da samun kwararar ƴan ci rani cikin Amurka daga Mexico, inda lamarin har ya fi na shekarar 2021. Fiye da ƴan ci rani 50 ne suka mutu a watan Yuni, a cikin wata babar mota da ta maƙale a kan babban titin Texas: shi ne lamari mafi muni na mutuwar ƴan cira ni da aka taɓa samu a Amurka.