2022 Mai Bankwana Na Daga Cikin Shekarun Da Ba A Samu Sauyi Mai Ma’ana Ba A Najeriya
Kogo Umar na bitar muhimman abubuwan da su ka wakana a shekarar ta bangaren siyasa, tattalin arziki, tsaro, ‘yancin dan-adam da sauran su.

Lauyan wanda kan yi sharhi kan lamuran yau da kullum ya ce an kara samun tabarbarewar lamura ne a shekarar in an kwatanta da shekarun da su ka gabata.

Hatta a majalisa ya ce ta nemi makudan kudi don gyaran tsarin mulki amma ta kare ba wani abun azo a gani da ta samar.

A bangaren siyasa ma koma baya a ka samu inji Barista Umar don yanda ‘yan takara kan dau salon kushe juna da miyagun kalamai.

Da a ka tambaye shi laifin shugaban kasa ne ko jami’an gwamnati ne da a ka dorawa alhakin kula da sassa?

Barista Umar ya amsa da cewa ai kifi daga kai ya ke baci don haka gazawar ta shugaban kasa ne don hakkin sa ne zuba ido kan yanda kasa ke tafiya da kuma wadanda ya damkawa amana.

Kawo wannan batu na mai laifi ya sa lauyan ya ce gwamnatin Buhari ce ta farko da ba ta taba sauya ministoci ba duk da rashin sakamako mai kyau da a ke gani.

Ga zaben 2023, Barista Umar ya ce lokaci ne da kowa zai zama alkalin kan sa, in ya gamsu da abun da gwamnati ta ke yi ya zabi dan takarar ta in kuma bai gamsu ba ya zabi wanda ya ga ya dace a cikin ‘yan takarar adawa.

Saurari rahoton:Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like