Hukumar yansanda jihar Jigawa sun kama yanfashi kuda hudu wayanda suke zargi su ne suke adabar karamar hukomomi bakawai a jihar.dan sandan jami’in hulda da jama’a,Mr. Abdu Jinjiri ya bayana hakane a yau juma’a a garin Dutse bayan ya bayana wa yan jarida yan fashin.ya bayana sunayen su kamar haka,Musa Muhammed, 26, Babannan Sale, 37, Inusa Sale 28 and Zakari Ya’u 32.
Jinjiri yace yanfashin suna sa kayan sojoji yayin da suke aiki da suka saba a kan hanyan Gujungu-Hadejia, Gumel-Maigatari da Gumel-Kano.ya kara da cewa sun samu nasarar kama yanfashin ne dalilin kara karfin patrol da kula da kuma nuna hikima wajen zagaye wuraren da suka tabatar yanfashin ke yin fashi.
Me maganan ya kara da cewa sun samu bindiga pistol guda biyu,harshashai guda bakwai da wandon da karamar rigar sojoji guda daya.Jinjiri yace yanfashin sun basu bayanai da zasu taimaki yansandan wajen kama raguwar yanfashin baki daya.
Yace karkashin umarin commissionan yansandan Jihar,Mr. Henry Fadairo, sun dau alkawarin kawar da duk wasu bata garin Jihar Jigawa.