Hukuma mai yaki da yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa, EFCC, ta ce, tana neman tsohon gwamnan jihar Katsina Ibrahim Shehu Shema ruwa a jallo.
EFCC ta sanya sanarwar ne a shafukanta na Internet, a inda ta ce “duk wanda yake da labarin wurin da tsohon gwamnan yake, to ya sanar da ita da gaggawa.”
Sanarwar ta ce hukumar EFCC ta dade tana ta faman gayyatar tsohon gwamnan amma yaki amsa gayyatar.
Hukumar ta ce tun watan Disambar 2015 take neman Shema amma hakan ya faskara.
EFCC dai ta ce tana zargin Ibrahim Shehu Shema ne dai bisa zuga kudaden kwangila da suka wuce kima.
sauran laifukan sun hada da barnatar da dukiyar al’umma da yin amfani da mukaminsa ta hanyoyin da ba su da ce ba.
Yanzu dai hukumar EFCC tana rokon jama’a da su shaida mata duk inda tsohon gwamnan yake.
Gwamnatin jihar Katsina karkashin gwamna Aminu Bello Masari dai tana zargin tsohon gwamnan da sace makuden kudade daga baitul malin gwamnatin jihar.
Sai dai kuma tsohon gwamnan, Ibrahim Shema da magoya bayansa sun sha musanta zargin.
Karin bayani
Tun dai lokacin da shugaba Muhammadu Buhari ya hau kan karagar mulki, ya lashi takobin kawar da rashawa da cin hanci, a kasar.
Kuma hukumar ta EFCC ce kan gaba wajen binciken mutanen da ake zargi da almundahana idan kuma an same su da laifi a gurfanar da su a gaban kotu.
Kawo yanzu dai za a iya cewa hukumar ta gayyaci kusan mafi yawancin gwamnonin jihohi 36 na kasar domin amsa zarge-zargen da ake yi mu su.
A mafi yawanci, jama’a ne ke rubuta takardun korafi kan tsaffin gwamnonin zuwa ga hukumar ta EFCC.
Sai dai kuma wasu na cewa wasu ‘yan jam’iyya mai mulki ne wato APC, suke yi wa ‘yan jam’iyyar adawa ta PDP shune.
Tuni dai jam’iyyar ta APC da hukumar EFCC suka musanta hakan.
EFCC
Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ne dai ya kafa hukumar EFCC a shekarar 2003.
Hakan ya biyo bayan kaurin sunan da Najeriya ta yi wajen satar kudade a fidda su zuwa waje, a idanun duniya.
To sai dai ko a lokacin ma wasu na yi wa hukumar kwallo irin na ‘jeka-na-yi-ka’, bisa zargin cewa shugaba Obasanjo na sanya EFCC kama duk wanda ba sa ga maciji da shi.
Ko a lokacin shugaba Goodluck Jonathan ma, hukumar ta sha irin wadannan soke-soke.
A baya-bayan nan, sabon shugaban Kungiyar Lauyoyi ta Kasa, Mahmoud Abubakar ya nemi da a rage wa EFCC karfin da take da shi.
Al’amarin kuma ya janyo musayar yawu tsakanin hukumar da Kungiyar Lauyoyin ta Kasa.