Turawan Yamma da hadin gwiwar hukumar yakar safara ta mutane a Najeriya na can na nazarin sabbabi na dabaru na rage radadin matsalar da ke neman tsallakawa har ga siyasa a cikin kasashen Turai.

Duk da cewar dai Tarrayar Najeriyar na zaman kasa ta farko a cikin nahiyar African da ta yi nasarar kafa dokar yakar safara ta mutane shekaru13 baya, har ya zuwa yanzu dai ta dau lambar zinari ta yawan ‘ya’yanta da ke haurawa ya zuwa Turai ko dan cin rani ko kuma sana’a ta karuwanci a kasashen Turai.
Wata sabuwar kiddigar Tarayyar Turai dai ta ce kasar ce ke da mutane sama da1300 a cikin kusan 22,000 da aka kai ga rijista ta zamo wa bakin hauren da aka ci zarafinsu a Tarrayar Turan, baya ga kuma dubban daruruwa na ‘yan kasar da kan yi kokarin tsallaka teku da nufin neman sabuwa ta rayuwa a tsakanin Turawan a duk shekara a fadar Richard Young da ke zaman mataimakin babban jakada na kasashen Turai a Tarrayar Najeriya da kuma ya ce hada karfi da karfe na zama na wajibi da nufin kai karshen matsalar.

“A kwai mutane tsakanin Dubu dari takwas zuwa miliyan guda da ake safararsu tsakanin kasashe na duniya a duk shekara, wannan kiyasi ne babba.”
Tuni dai manya na kawayen suka yanke shawarar bullo da sababbi na dabarun da suka hada da wani sabon gangami na wayar da kan al’umma musamman ma a Jihohin Edo da Delta da Akwa Ibom da Benue da kuma Imo da ke zaman na kan gaba kan matsalar matasan da ke kokarin zuwa Turai.
Alhaji Abdurazak Dangiri dai na zaman shugaban hukumar yakar safarar mutane a cikin Tarrayar Najeriyar.Kuma a fadarsa dabarun kaiwa ya zuwa yaran na zaman kokari na kare matsalar tun daga farkonta.