Farashin dala a kasuwar canji ya sauka zuwa Naira 454 a yau sakamakon umarnin da Babban bankin Nijeriya CBN ya bayar ga ‘yan kasuwar canji kan farashin da CBN din ke son ‘yan kasuwar su sayar da dala
CBN ya bayyana cewa yana sayar da dala ga ‘yan canji a kan Naira 375, a saboda haka ta bayar da umarni da kada farashin dala a bakar kasuwa ya shige Naira 385
A makonnin da suka gabata ne dai farashin dala ya yi tashin gwaron zabi inda har aka sayar da dala a kan Naira 490 da ma sama da haka, inda aka sayar da fam din Burtaniya akan Naira 601
Sai dai, shugaban kungiyar ‘yan canji ta kasa ABCON, Alhaji Aminu Gwadabe, ya danganta tsadar da dalar ta yi ga bukatar da ya karu ba wai kawai daga cikin gida Nijeriya ba, a’a, har daga kasashen da muke makwabtaka da su
Alhaji Gwadabe ya ci gaba da cewa, kasashen Chadi da Benin sun krkato da bukatar dalarsu zuwa ga Nijeriya. Haka kuma a wancan lokaci mun ga ‘yan China da dama suna neman dala a cikin Nijeriya don aiwatar da kasuwancinsu. Wannan ya sa bukatar dalar ta karu, wanda hakan kuma ya haifar da tsadarta
Amma zuwa yanzu, Naira ta farfado sakamakon bullowar wani kamfanin canji da ake kira da Travelex da ya zo ya ke bayar da canji a farashi mai sauki
Wannan ya sanya Naira ta kara daraja a ‘yan kwanakin nan daga Naira 490 a kowace dala zuwa Naira 455 a kowace dala