Buhari: Ina da sauran gwaje-gwaje a yan makonni kadan masu zuwa.


buhari

 

 

Shugaba Muhammadu Buhari ya dawo gida Najeriya yau da safe bayan da ya shafe kwanaki, yana jinya a birnin London, Shugaban dai yace bai taba yin rashin lafiya irin wannan ba, ko da a lokacin da yake cikin aikin soji.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a lokacin wani taro na mintuna 30 da aka shirya masa a fadar mulki ta Aso Rock jim kadan bayan dawowarsa.

Buhari yace na dawo yaune don na huta shikuma Osinbajo ya cigaba da aiki.

Har ila yau shugaban yaci gaba da cewa haryanzu yana da sauran gwaje-gwaje da za ayi masa a makonni kadan masu zuwa.

You may also like