Aƙalla Ɓarayi 3000 Ne Suka Miƙa Makamai A Zamfara


Rahotanni daga jihar Zamfara sun tabbatar da cewa kimanin barayi 3000 ne suka mika makamansu a karkashin wani shirin afuwa da gwamnatin jihar ta kaddamar.

Da yake karin haske kan shirin, Shugaban Majalisar Dokokin Jihar, Sanusi Rikji ya ce daga shekarar 2011 zuwa yanzu, mutane 1,321 suka rasa rayukansu kan ayyukan barayin yayin da wasu mutane 1,881 suka samu raunuka. Ya ce, haka ma, an sace Motoci da babura 185.

You may also like