Ba dukkanin mai karatu bane zai iya tuna lokacin da aka ga shugaban ƙasa Muhammad Buhari da kuma Ayo Fayose gwamnan jihar Ekiti suna gaisawa ba a bainar jama’a. Watakila mutanen biyu suna kaucewa haɗuwa da juna.
A karshe dai mutane biyun sun haɗu ranar Alhamis a taron majalisar ƙasa da shugaban kasa Muhammad Buhari ya jagoranta inda suka gaisa da juna.
Fayose wanda za a iya bayyanawa da mutumin dake kan gaba wajen sukan
shugaban kasa Muhammad Buhari tun kafin zaɓen shekarar 2015 Fayose yake shugaban Buhari lokacin da yake ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyar APC.