A Daina Aibata Mata Saboda Abinda Maryam Sanda Tayi – Fadila H Aliyu KurfiZuwa ga mazan Facebook YA ISA HAKA, laifin Maryam Sanda ya tsaya kanta ita daya, kuna aibanta mata kuna zaginmu kan laifin wata wanda ko wurin ubangiji ita kadai zai hukunta ba mata duka ba, wacce bata da goyon baya daga gare mu mata .

Mace nawa ce rungume da mijinta sai dai mutuwa ta raba, da dadi ko kuma akasinsa, a cikin ciwo ko lfy, karamin misali duba mahaifiyarka ko yan  uwanka mata sun kashe mazansu?

Maryam Sanda ta wakilci kanta ne ba mata ba, wasu don wuce makadi da rawa wai ba za su auri mai suna Maryam ba sbd wata Maryam da ta kashe mijinta, wani gwani na gwanayen ma dauko wani shirmen reference dinsa ya yi wai Maryam hudu ya sa ni wacce ta kashe mijinta, to ya lissafa dubban Maryam din da ya sa ni zaune lafiya a dakinta.

Idan kuma duk zuriyarsu babu wata Maryam da take zaman aure lami lafiya bari na baka misali da kakata, “Maryam ko ace mata Mairo ko da fillaci ace Bingel kyakkyawar bafullata nake wacce ta yi zamani a lokacinta, jikin mai boye tsufa ne, ta rasu tana da shekara kusan casa’in da doriya, amma har ta rasu furfurar kanta kadan ce kanta duk bakin gashi ne.

Kamar lokacin zafi tsofaffi na shan iska basa saka riga amma ban ita sbd kirar da Allah ya bata kamar budurwa ‘yar shekara sha biyar, duk wanda ya kalleta sai ya kara duk da tsufanta, mijinta ya rasu tun tana da kuruciyarta bata wuce aure ba kuma tana da tarin masoya sbd da kaunarsa bata kuma aure ba, ita burinta shine ita ma ta mutu a matsayin matarsa kamar yanda ya mutu a matsayin mijinta rungume akan kafarta, kasan labarinta? Amsar a’a sbd ita alkhairi ta yi, ku kuma baku yada shi.

Idan Maryam Sanda ta bata maka har kana condemning duk wata Maryam ya zaka yi da hakkin wasu Maryamomin, ina Nana Maryama mahaifiyar Annabi Isa, thousands of Maryama suna gidan mazajensu.

Ke nan kai da ma su tunani  irin naka kun yi condemning  mai asalin sunan Nana Maryama baiwar Allah. Da sauran bayin Allah masu irin sunan da su ka yi dedicating life dinsu ga aure da rayuwar yaransu, simply don sunan Mom dinka ko yar uwarka ba Maryam ba ne, wani ma bincike ya hau yi wai ma su sunan Maryam hudu suka ta6a kashe mazajensu. Wani sunansa Abubakar sunan shugaban ‘yan boko haram, ke nan sai mu ce ba mu kuma auren mai irin sunan sbd ya mayar da dubban mutane marayu.

Wani kuma ma ” Wai matan Arewa abin tsoro ne bari mu  guje ku” sai me? Ku guje mu mana! Kamar iyayenmu mata su ba ‘yan Arewar ba ne,  kuma ba su yanke mana iyayenmu maza ba, duk millions of matan arewar da su ke zaune lafiya a gidajensu su ba mata bane, sai Maryam Sanda, maza nawa ne suka kashe matansu? Kun san adadi? Mu fasa auren  mu ka yi?

Kai maza! Abin da Maryam ta yi is very wrong, dole ta fuskanci hukunci, abin da ta yi ba kishi bane rashin imani ne, ba soyayya bace akasinta ce, duk wanda kake so da gaskiya baka iya jurar ganin jininsa na gudana yana neman taimako kuma taimakonka ka saka masa idanu,ka kashe shi da kanka, idan kun kira wannan kishi ko soyayya to akwai gyara,  kuma mata basa bayanta abar dora mana laifi. A yanke ma Maryam hukunci, RAI A BAKIN RAI NE, Bilya mace fa ta haife shi, shin baku tunanin mata na jin kuna da takaicin kasan gilla ma dan su.

Mace miliyan nawa ke aure sai don wasu tsiraru wakilin shedan sun yi laifi a rika mana kudin goro, ni fa a Facebook kamar na hunce mu daku da wasu sbd abin haushi, ku zagi Maryam ko kuma ku cigaba da tsinar mata iyayenmu. Wurin ai banta mata mutun ya rika kokari keta haddin mahaifiyarsa tunda ita ma ai mace ce.

Da za a turo Maryam gaban mata sai sun yi gutsi-gutsi da ita, mun tsine mata mun ai bantata amma still zunubinta na kokarin shafar mata, to ko wurin Allah laifinta baya shafarmu, duk wanda ya zagi mace wlh bai yi tunani ba, masu mummunan kishi wakilan shedan ne, kara kishiya Allah ya halasta ma maza,  babu wacce ta isa ta hana, ranar da Maryam ta yenke Bilya ranar an yo ma wata kishiya kuma bata so amma dole ta hakura.

You may also like