A Gaggauta Gurfanar Da Tukur Mamu Gaban KotuABUJA, NIGERIA – Da yake yanke hukunci kan karar da lauyoyin Mamu suka shigar na ci gaba da tsare wanda suke karewa, mai shari’a Edward Andow ya umarci hukumar DSS da ta tabbatar da gurfanar da Malam Mamu gaban shari’a don tantance ko shin ya aikata wani laifi ko a’a.

Yau dai kusan watanni biyar kenan DSS ke tsare da Malam Tukur bisa zargin shiga tsakani yayinda ‘yan bindiga suka yi garküwa da fasinjojin jirgin kasannan da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna.

Tuni kuma lauyan dake kare Mamu, Battista Muhammad Sani Katu S.A.N. ya nuna gamsuwa da wannan hukunci yana mai cewa dama su abin da suka bukata daga kotun kenan.

Malam Tukur Mamu

Malam Tukur Mamu

Lauyan wanda ya ce Tukur Mamu bai da Lafiya, koda yake hukumar ta DSS tana bashi kula sosai, ta ma kai shi asibiti, amma ya ce su sun dai fi bukatar a gabatar da shi gaban kotu don a saurari shari’ar.

Tuni kuma masana tsarin mulki irinsu Barrister Yakubu Sale Bawa ke ganin hukumar DSS ko dai ta gurfanar da shi gaban kotu ko a bada shi beli ganin irin lokacin da ya dauka a tsare.

Ya ce da yake tunda farko hukumar tsaron ta nemi kotu ta bata damar ci gaba da tsare Mamu na watanni biyu, inda wa’adin ya kare, yana mai cewa duba da irin lokacin da ya share a tsare, to bisa ga kundin tsarin mulkin Najeriya yanzu babu wata dama ba neman izinin kotu don ci gaba da tsare shi.

Barrister Bawa ya ce yanzu dai abin da ya rage wa DSS shi ne ko dai ta gurfanar da shi a gaban alkali, ko a bada belinsa, domin duk wani yunkurin ci gaba da tsare shi tamkar yin karan tsaye ne ga tsarin mulki.

Kokarin da Muryar Amurka ta yi don jin ko me Gwamnatin Najeriya zata ce akan wannan hukunci bai yi nasara ba.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like