A Gobe Ake Sa Ran ‘Yan Shi’a Zasuyi Tattaki A Jihar KanoAlmajiran Malam Ibrahim Zazzaky reshen jihar Kano sun bayyana yin tattaki gobe Lahadi a jihar Kano. Sanarwar ta fito daga bakin Malam Sunusi Abdulkadir a yayin taron manema labarai da aka yi a sakatariyar kungiyar ‘yan jaridu ta kasa reshen jihar Kano. “Manufar wannan taro domin mu sanar da al’ummar jihar Kano da jami’an tsaro cewa, gobe Lahadi za mu fita taro da muka saba duk shekara, wanda aka fi sani da Tattaki. 

Domin taya ahalin gidan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam juyayi da wahalhalun da suka sha a waki’ar Karbala. Shine ya sa Musulmi ‘yan Shi’a ke tattaki domin dandana wannan wahala da suka sha. Kuma kuma ‘yan jaridu shaida ne na cewa, muna yin taron lafiya mu gama lafiya”.

A yayin amsa tambayoyi, an tambayi Malam Sunusi Abdulkadir cewa, kusan wannan tattaki suna yi ne zuwa gidan jagoransu Malam Ibrahim Zazzaky a Zariya kuma a halin yanzu baya nan. Ko ina suka nufa wannan karon. Sai ya amsa da cewa, “Ba lallai ne gidan Sheikh Zazzaky kadai muke zuwa ba, a Hussainiya muke taruwa, kuma wannan karon ba Zariya za mu je ba, wani waje za mu yi tattaki a yi addu’a kowa ya tafi”. 

Da aka kara tambayarsa dangane da sanarwar jami’an tsaro na hana irin wadannan tarukan, sai ya ce ba da su ake ba. Domin zuwa yanzu ana taro a Masallaci da Coci kenan ba taron addini aka hana ba. Kuma baya ga haka kundin tsarin mulkin kasa ya ba wa kowane dan kasa ‘yancin yin addini.

You may also like