A Gobe Ne APC Zata Cinma Matsaya Kan Zaben Shugabannin Jam’iyyar


A gobe Litinin ne, jam’iyyar APC za ta gudanar da taron babban kwamitin gudanarwarta don cimma matsaya kan yadda za ta gudanar da zaben shugabannin jam’iyyar.

Rahotanni sun nuna cewa a halin yanzu Gwamnan Kano, Umar Ganduje na tuntubar shugabannin APC na jihohin Arewa don goyi bayan Shugaba Buhari na dakatar da batun tsawaita wa’adin shugabannin jam’iyyar.

Haka ma, Gwamnan Oyo, Abiola Ajimobi ya nemi hadin kan shugabannin yankin Yarbawa sai kuma Gwamnan Imo, Rochas Okorocha wanda ke tuntubar shugabannin yankin Kudu maso Gabas inda gwamnonin suka shugabannin tabbacin sake komawa kan kujerunsu idan an yi zabe.

You may also like