A Gobe Ne Kungiyar Malamai Za su Fara Yajin Aiki A Kaduna Kungiyar Malamai reshen jihar Kaduna za ta fara yajin aiki a gobe Litinin don nuna rashin amincewa da matakin da gwamnatin jihar ta dauka na sallamar malaman makarantar Firamare har 21, 780 bayan sun fadi wata jarrabawar kwarewa kan harkar koyarwa da aka shirya masu a watan Yuni da ta gabata.

Kungiyar ta nuna cewa bin matakin ya zama dole kasancewa gwamnati ta yi fatali da wa’adin makonni biyu da kungiyar ta ba gwamnati na janye wannan shiri na sallamar malaman makaranta inda ta fara raba masu takardar sallama bayan da aka dawo hutun sabuwar shekara.

You may also like