A goge KWANKWASIYYA a gine-ginen Gwamnati. 


Majalisar dokokin jihar Kano da ke arewacin Najeriya, ta zartar da wani kuduri da ya nemi a soke sunan Kwankwasiyya daga gine-ginen gwamnati.
Majalisar ta kuma nemi a sauyawa rukunin gidaje da aka yi wa lakabi da Kwankwasiyya da Amana da kuma Bandirawo suna, a inda ta nemi da a sanya musu sunayen malaman addini.

A zamanta na ranar Larabar nan, majalisar ta amince daa sanyawa rukunin gidajen Kwankwasiyya suna Shaikh Jafar Mahmud Adam.Shi kuma rukunin gidajen Amana zai amsa sunan Shaikh Nasuru Kabara, a inda Bandirawo zai koma Khalifa Shaikh Isyaka Rabiu.

Majalisar ta kuma ce a goge duka sunayen”Kwankwasiyya” daga jikin gine-ginen gwamnati, da aka rubuta a lokacin da Rabiu Musa Kwankwaso ke gwamnan Kano.

Shugaban masu rinjaye na majalisar ta dokokin jihar Kano, Hon. Yusuf Abdullahi Ata ya shedawa ‘yan jaridu cewa,sun dauki wannan mataki ne saboda bai dace a rinka rubuta sunan wata kungiyar siyasa a kan ayyukan gwamnati ba.

To sai dai wasu ‘yan majalisar kamar Zubairu Mamuda Madobi da ke goyon bayan Kwankwaso, sun ce ba sa goyon bayan matakin takwarorin nasu, kuma sun yi Allah-wadai da kudirin.Su dai suna ganin wannan wani bita da kullin siyasa ne ake yiwa Rabiu Musa Kwankwaso.

A baya-bayannan dai dangantaka ta yi tsami tsakanin gidajen siyasar gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, da kuma wanda ya gada Rabiu Musa Kwankwaso.

You may also like