Jami’an tsaro a Maiduguri sun harbe wani dan ƙunar ɓakin wake mai shekaru 13, a kusa da jami’ar Maiduguri.
Wata majiya ta shedawa jaridar The Cable cewa jami’an tsaro ne suka harbe ɗan kunar baƙin wake lokacin da yake ƙoƙarin shiga harabar jami’ar ta ɓarauniya hanya.
“Ƙarar da kaji ƙarar bom ɗin dake jikin ɗan ƙunar baƙin waken ne bayan da muka harbeshi ya fadi. Ya zuwa yanzu ɗan ƙunar baƙin waken ne kaɗai ya mutu,” majiyar tace.
Ibrahim Jidda wani ɗalibi a jami’ar ya shedawa The Cable cewa fashewar abun ya kawo ruɗani a Jami’ar.