A Ina Gizo Ke Saka Tsakanin Masanin Gargajiya Da Na Asibiti?
In ka debe zuwa awun ciki da haihuwa a asibiti da ke samun karbuwa, sauran bukatun jinya musamman a karkara in ba ya gagara ba mutane da dama kan yi amfani da magungunan gargajiya.

Baya ga kasancewa magungunan gargajiya na da araha da saukin samu, wasu mutane kan dau wasu cutukan ma na gargajiyar ne don haka maganin su sai ta hanyar gargajiya.

Malaman lafiya na cewa sanin cuta da bin ka’idojin yadda za’a dakile ta shine magani.

A kullum marasa lafiya na fadi tashin neman magani don samun waraka.

Amma abin tambaya a nan shine, A ina gizo ke saka tsakanin masanin gargajiya da na asibiti?

Akwai bambamcin ra’ayi ga masu amfani da maganin gargajiya ko na asibiti, kamar yadda suka bayyana.

Sau tari mutane kan sha magani ba tare da shawarin likita ba, yayin da a ke shan maganin gargajiya ba tare da kayyade ma’aunin mazubi ko yawan da za’a sha ba.

Kwararren likita Dr. Lawal Musa Tahir na asibitin Nizamiye a Abuja ya ce akwai illolin dake tattare da shan magani ba bisa ka’ida ba.

Idan za’a iya tunawa hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Najeriya NAFDAC, ta yi gargadi kan shan maganin ganye don gujewa yawan mace-macen da za’a iya kaucewa.

Saurari rahoton:Source link


Like it? Share with your friends!

-1

You may also like