A yayin da ake ci gaba da zaman dar dar da sace mutane da yin garkuwa dasu domin kudin fansa a Najeriya, wannan matsala na cigaba da bazuwa tamkar wutar daji a jihohin kasar.
Wani amininsa daya nemi a sakaya sunansa ya ce yana zaune a gida sa sai aka kira lambar wayarsa aka fada masa cewar ga halin da amininsa ke ciki wato anyi garkuwa da shi.
Malamin ya kara da cewa sun tattauna da mutanen da suka sace aminin nasa kuma ya basu abinda suka bukata amma har zuwa lokacin da wakilin sashen Hausa ya tattauna da shi malamin wanda yace kwanaki goma sha tara Kenan amma haryanzu ba labarinsa.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Taraba CP Yakubu Yunana Babas ya bayyana cewa jami’an ‘yan sanda sunyi artabu da wasu masu sace mutane domin kudin fansa har sun sami nasarar hallaka uku daga ciki.