A karo na biyu babban sifetan yan sanda ya gaza bayyana gaban majalisar dattawa


Ibrahim Idris, babban sifetan yan sandan Najeriya ya gaza bayyana a gaban majalisar dattawa karo na biyu cikin mako guda.

Majalisar dattawa ta gayyace shi domin ya yi mata bayani kan yadda ake zargin cin zarafin sanata Dino Melaye.

Haka kuma majalisar ta gayyace shi ya yi mata bayani kan kashe-kashen dake faruwa a sassa daban-daban na kasarnan.

Kamata ya yi Idris ya bayyana a gaban kwamitin a makon da ya wuce amma bai yi haka ba inda ya raka shugaban kasa, Muhammad Buhari ziyarar aiki da ya kai jihar Bauchi.

Hakan ya harzuka yan majalisar inda suka nemi lallai ya bayyana a ranar Laraba amma sai ya tura naibinsa, Joshak Habila ya wakilce shi.

Ya bada uzurin cewa yana wata ziyarar aiki a Kaduna da ta danganci matsalar tsaro.

You may also like