A Karon Farko A Tarihi Mata A Saudiya Za Su Fara Tuka Mota 


A Karon farko a tarihi an bawa mata yan kasar saudiya damar su tuka mota.

A cewar  kamfanin dillancin labarai na kasar ta saudiya SPA, tuni aka zartar da wata doka da zata bawa maza da mata damar mallakar shedar izinin tuki. 

Ma’aikatun gwamnati zasu rubuta rahoto cikin kwanaki 30 kafin a aiwatar da dokar a watan Yuni na shekarar 2018.

Kafin dai a bada wannan umarni kasar ta saudiya ce kasa daya tilo a duniya da mata basa tuka mota.

Kungiyoyin kare hakkin mata sun dade suna fafutukar ganin an bawa mata damar tuka mota a kasar.

A shekarar 2011 sai da aka kama Manal al-Sharif wata mai fafutukar kare hakkin mata bayan da ta dauki fefan bidiyo na kanta tana tuka mota kafin daga bisani ta saka a shafin Intanet na YouTube.

Bayan da aka sako ta, Al-sharif ta ci alwashin cigaba da nemawa mata yancinsu. 

Ko a makon da ya gabata sai da wani Malamin addinin musulunci dake kasar ya bayyana mata a matsayin mutane masu karamar kwakwalwa inda yace hakan ne yasa ba a basu damar tuka mota ba.  

 

You may also like