Shahararren kamfanin yin lemun kwalba na Coca cola ya bayar da sanarwar cewa zai fara yin giya a karon farko tun bayan shekaru 125 da kafa kamfanin.
A cikin sanarwar da ya fitar, kamfanin ya nuna cewa zai fara yin giyar ce a kasar Japan a bisa la’akari da yadda yawan wadanda ke shan barasa a kasar ke karuwa.