A Karshe, Jami’an Tsaro Sun Cafke Sanata Dino Melaye


A karshe dai, rundunar ‘yan sanda ta samu nasarar cafke dan majalisar Dattawan nan mai wakiltar Jihar Kogi ta Yamma, Sanata Dino Maleye bisa zargin daukar nauyin ayyukan ta’addanci a jiharsa.

Rahotanni sun tabbatar da cewa a yau Litinin ne aka cafke shi a filin saukar jiragen sama na ” Nnamdi Azikwe” da ke Abuja a kan hanyarsa na zuwa kasar Moroko. ‘Yan sanda dai sun jima suna farautarsa wanda a wata ziyara da ya kai jihar Kwara sai da ‘yan Banga suka bashi kariya ta yadda jami’an tsaro suka kasa kama shi.

You may also like