An mika rahoton kasafin kudin shekarar 2018 a gaban majalisar dattawa bayan an samu tsaiko.
Shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar,Danjuma Goje shine ya ajiye rahoton kasafin kudin a gaban majalisar.
Majalisar dattawan ta yi alkawarin zartar da kasafin kudin a ranar 24 ga watan Afirilu amma hakan ta gaza tabbata.
A ranar 3 ga watan Mayu majalisar wakilai ta yi nata alkawarin na zartar da kasafin kudin a mako mai zuwa.
Amma kuma ba mika rahoton kasafin kudin ba a dukkanin majalisun biyu, majalisar dattawa ba ta zauna ba a ranar Alhamis ta wancan makon.