A karshe ‘yan sanda sun dauki Dino Melaye ya zuwa Lokoja


A karshe jami’an yan sanda sun samu nasarar daukar sanata Dino Melaye ya zuwa Lokoja babban birnin jihar Kogi inda suka gurfanar da shi gaban kotu.

Ana dai tuhumar Melaye da laifin hada baki wajen bawa yan daba makami domin su aikata fashi da makami da kuma yin garkuwa da mutane.

An dauki Melaye ya zuwa Lokoja cikin wata motar daukar marasa lafiya mallakin rundunar yan sandan Najeriya.

Tun farko Melaye ya bayyana damuwarsa kan cewa rayuwarsa tana cikin hatsari kuma za a iya kashe shi idan har ya gurfana a gaban kotu a jihar Kogi.

A ranar Laraba ne yan sanda suka sake kama sanatan baya wata kotu dake Abuja ta bayar da belinsa kan kudi naira miliyan 90 da kuma wasu mutane biyu da za su tsaya masa.

Amma yan sanda sun dage kan cewa belinsa da kotun ta bayar bai shafi tuhumar da ake masa ba tun da fari saboda haka dole ya gurfana a gaban gaban kotu.

You may also like