A Mulkin Najeriya Kowa Yaji A Jikinsa Yanzu –  Sanata Makarfi 



An bayyana cewar a halin da ake ciki yanzu a tarayyar Nijeriya basai an fadiba kowa yaji a jikinshi, sannan jama’a zasu cigaba da dandana kudarsu har sai idan an samu sauyi na gaskiya da gaskiya ba canjin yaudara ba.
Shugaban jam’iyyar PDP na kasa baki daya tsohon gwamnan jihar Kaduna Alhaji Ahmad Muhammad Makarfi ya bayyana hakan, lokacin daya tarbi bakuncin gamayyar kungiyoyin cigaban matasan arewa, wadanda suka kawo mishi ziyara a gidanshi dake garin Kaduna.
Sanata Makarfi ya cigaba da cewar, yawan ‘yan Nijeriya sunyi zabe a shekarar 2015 da niyyar su kawo canji domin samun saukin al’amurransu, amma abin takaici shine sai gashi wadanda aka zaba din sun yaudari jama’a ta hanyar jefasu cikin talauci, su kuma a hannun guda suna facaka da dukiyar gwamnati.
Shugaban PDP din ya kara da cewar dolene a garesu su mike domin fasalta jam’iyyar tasu ta PDP yadda zatayi nasarar kwace mulki a shekarar zabe ta 2019, sannan ya bayyana cewar dolene a gabatar da batun taimakawa jama’a kafin batun jam’iyya, domin hakan yana daga cikin sakamakon rahoton daya amsa daga hannun shugaban kwamitin fasalta jam’iyyar PDP Farfesa Jerry Ghana, sannan kuma dolene a kyautatawa al’ummar wuri, ba aje a kwaso baki daga waje a sanyasu a madafun ikon jiha, sannan ‘yan asalin jiha na cikin ukuba.
Tunfarko da yake gabatar da nashi jawabin, shugaban gamayyar kungiyoyin cigaban matasan arewacin Nijeriya Alhaji Imrana Nas wanda akafi sani da suna shugaban talakawa, ya bayyana cewar makasudin ziyarar tasu shine, domin su jinjinawa shugaban bisa ga irin kokarin da yake nunawa wajen taimakawa matasan yankin arewa, sannan ya kara isar da sakon matasan arewa gareshi na a cigaba da tafiya tare dasu, ba’a ci moriyarsu ba sannan a watsar dasu.

You may also like