A Takaice: Ashe Ba Maciji Ba Ne Ya Haɗiye Naira Miliyan 36 A Ofishin JAMB Ba


Bayan wadda ke da alhakin kula da kudin JAMB dake jihar Benue, Misis Philomina Chiese ta bayyana a gaban hukumar EFCC, ta yi amai ta lashe, inda ta ce ba maciji bane ya hadiye kudin, wani na gaba da ita ne a ma’aikatar mai suna Samuel Umoru ya yi babakere da kudin.

You may also like