A waɗanne ƙasashe za a yi azumi mafi tsawo ko gajarta a duniya ?.

Sama da Musulmai miliyan dubu ɗaya ne suka fara azumi a faɗin duniya a wannan makon, inda za su shafe tsawon wata guda suna azumin na watan Ramadana.

Azumin wanda ake fara shi daga lokacin sahur a sauke shi bayan faɗuwar rana ana yin shi ne na tsawon sa’a 12 zuwa 18 a ko ina a faɗin duniya, amma hakan ya danganta da wanne saƙo mutum yake zaune a duniya.

Musulmai da dama a duniya sun yi amannar azumin Ramadana na ɗaya daga cikin ginshiƙan abubuwa biyar da addinin Musulunci ya kafu a kansu, tun lokacin Annabi Muhammad (SAW)sama da shekara 1,400 da suka gabata.

Lokacin azumi ana nesantar cin abinci da sha da duk wani abu mai alaƙa da saduwa tsakanin namiji da mace daga lokacin da aka yi sahur har zuwa faɗuwar rana.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like