A Yau Ne Buhari Zai Karbi Ragamar MulkiFadar Shugaban kasa ta tabbatar da cewa a yau Litinin ne, Shugaba Muhammad Buhari zai sanar da majalisar tarayya cewa zai karbi ragamar mulki daga hannun Mataimakinsa wanda ke rikon kwarya kamar yadda doka ta tanada.

 
Kakakin Fadar Shugaban, Garba Shehu ya ce a bisa tsarin mulki sai Buhari ya rubuta wa majalisar tarayya bukatar komawa kan aiki bayan dogon hutun da ya dauka kamar yadda ya sanar da su tun da farko bisa tafiyarsa wajen duba lafiyarsa.

You may also like