Dan takarar gwamnan Kano da ke arewacin Najeriya na jam’iyyar NNPP, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana yadda zai inganta rayuwar jama’ar jihar.
A tattaunawarsa da BBC Hausa, dan takarar, wanda ake yi wa lakabi da Abba Gida-Gida, ya ce zai bai wa fannin ilimi da lafiya muhimmanci idan aka zabe shi.
“Mun fitar da manufofi na abubuwan da muke so mu yi wa al’ummar Kano idan Allah ya ba mu dama. A wannan lokaci na fadi abubuwa da dama musamman wadanda suka shafi fannin ilimi da harkar lafiya da harkar noma da kuma kyakkyawan yanayi da ya shafi shugabanci,” in ji dan takarar na NNPP.