Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin man fetur, ya shaidawa majalisar cewa gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari ba dan asalin jihar bane.
Yari da Marafa sun dade suna cece-kuce s kan wakilin da shugaban ƙasa Muhammad Buhari ya tura majalisar domin tantancewa a matsayin kwamishina a hukumar zaɓe ta kasa INEC da zai wakilci jihar.
Yayin da Yari ya dage kan cewa mutumin da shugaban ƙasar ya tura da sunansa gaban majalisar ba ɗan asalin jihar bane saboda haka bai dace majalisar ta amince da shi ba, shi kuwa marafa ya dage kan cewa sai an tabbata dashi.
Marafa ya shaidawa majalisar haka a ranar Alhamis lokacin da ya nemi majalisar ta amince da sunan mutumin da Buhari ya aike dashi gabanta.