Abdulaziz Yari Yayi Barazanar Zasu Kwashi Yan Kallo Da Hukumar EFCC  Kan Kudaden Biyan Bashin Paris Club  


Hoto:dailynigerian.com

Gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari yayi barazanar cewa zasu kwashi yan kallo da hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati ta EFCC, kan zargin da take masa na karkatar da kudaden biyan bashin Paris Club.

Gwamnan wanda shine shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya yayi wannan barazanar ne jiya Alhamis a Abuja lokacin da yake ganawa da manema labarai.

 Ana zargin Yari, da laifin karkatar da $500,000 da kuma naira miliyan  500  daga cikin kudin da aka biya jihohi 36 na biyan bashin kudin Paris Club da gwamnatin tarayya tayi, domin amfanin kashin kansa. 

Yace zai rubutawa gwamnatin tarayya takarda a hukumance domin mika korafi  kan halayyar shugaban riko na hukumar EFCC Ibrahim Magu akan sauran gwamnoni. 

” Zan rubutawa gwamnatin tarayya wasika cewa ya isa haka domin an kaimu bango, ko dai EFCC tayi aikinta ko kuma mu kwashi yan kallo,”yace. 

Yace yayinda gwamanoni a kungiyar suke goyon bayan yaki da cin hanci da rashawa da gwamnatin tarayya take amma kuma suna adawa da salon da hukumar take bi wajen yaki da wannan masifar ta cin hanci. 

Gwamnan ya shawarci hukumar ta EFCC kan ta maida hankali wajen yaki da cin hanci mamakon bita da kulli. 

 

You may also like