Tsohon shugaban kwamitin kasafin kudi a majalisar wakilai Abdulmuminu Jibrin ya ce shi da lauyoyinsa sun tafi kotu domin kalubalantar dakatarwar da majalisar ta yi masa, yana mai cewa babu gudu babu ja da baya.
Haka kuma ya shaida a wata hira da ya yi da kafar yada labarai ta BBC cewa ba zai taba janye zargin da ya yi wa Yakubu Dogara da wasu manyan ‘yan majalisar uku ba, na cewa sun yi yunkurin yin cushen Naira biliyan 30 a kasafin kudin shekarar 2016.
A jiya Laraba ne dai majalisar ta dakatar da dan majalisar na tsawon shekara guda (kwanaki 180 na zaman majalisa), bayan da ta same shi da laifin bata mata suna da karya ka’idojinta.
Haka kuma majalisar ta hana sa rike kowanne irin mukami har zuwa karshen wa’adinta, kuma ta bukaci ya rubuta takardar neman afuwa kafin ya dawo, bayan wa’adin hukuncinsa ya cika.
Sai dai Jibrin ya ce ya na nan a kan bakansa, ya ce ya na da shaidu da ke nuna cewa Dogara, da mataimakinsa Yusuf Lasun, da Alhassan Doguwa da Leo Ogor sun ware wa kansu Naira Biliyan 40 a cikin biliyan 100 da aka warewa gaba dayan majalisar dokokin tarayya ta Nijeriya.