
Asalin hoton, AFP
Shugaban Amurka Biden ya yi wa shugabannin Afirka jwabi a taron ƙolin da ƙasarsa ta jagoranta a birnin Washiginton DC
Da alama farin jinin Afirka a dan tsakanin nan yana neman zama kwatankwacin budurwar da ta yi goshin samari daga sassa daban-daban na duniya.
Kowacce kasa na kokarin kulla alakar kasuwanci a dan tsakanin nan, sun kafe cewa alaka tsakanin Afirka da kasashen waje mai karfi ce da babu mai shiga tsakani.
Abin da ya fito fili a nan shi ne yadda Washington ke kokawa da abokiyar takararta Chin a nahiyar Afirk, wani lokaci har da Rasha na kokarin shiga tsakani, to y yin da aka kammala taron kolin shugabannin kasashen Afirka batun abinda aka cimma a taron ke jan hankalin mutane.
A shekarun baya-bayan nan, Amirka na fadan karkashin kas da Beijing har wani lokacin da Rasha domin fin karfinsu kan Afirka.
Shugancin da ya gabata na shugaba Donald Trump, ya kare da tsamin alaka da zarge-zarge da korafe-korafe kan alakar China da Afirka.
A yanzu Amirka na kokarin yin wani abu da ke nuna sabon salo da tsarin shan gaban China, da Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro John Bolton zai yaye lalubensa.
Ya kuma yi batu kan bai son bata kudaden harajin miliyoyin dalolin da ake karba a hannun ‘yan kasa.
Sai dai abin da ya faru a makon nan, ya zo da ban mamaki saboda batun Bolton da abin da ka gani a zahiri sun sha banban.
Asalin hoton, Reuters/EPA
Shugaba Filipe Nyusi na Mozambique, Shugaba Muhammad Bazoum na Nijar, Shugaban Somalia Hassan Sheikh Mohamud, sai kuma Shugaban Rwanda Paul Kagame, duk an ba su damar yin jawabi a wurin taron
Da farko dai shugaba Joe Biden bai furta kalmar ”China” kai tsaye a cikin jawabin da ya yi wa shugabannin kasashen Afirka a ranar Laraba.
Sakataren harkokin wajen Amirka Anotony Blinkin ya dan yi hannun ka mai sanda, a lokacin ziyarar shi ta farko nahiyar Afirka, inda ya ke cewa : ”Tsarin da muke da shi a Afirka na ‘yan nahiyar ne ba na China ba.”
Duk da hakan, babu tantama kan kishin da ke tsakanin kasashen biyu, kuma hakan ya fito karara inda Amirka ke kara inganta harkokin lafiya, da muhalli, da makamashi mai tsafta da tsaro da uwa uba kasuwanci a Afirka.
Batutuwan da aka maida hankali a taron kolin sun hada da yaukaka dangantakar da dama ta na nan tsakani, da kara fadada wasu shirye-shirye da suka hada da:
- ci gaban Afirka – Amirka ta kirkiri inganta huldar kasuwanci tsakaninsu da aka fara tun shekarar 2018
- shirin zamanin Clinton na bukasakasuwancin Afirka da samun dama gare ta, ta yadda kayan da ake samarwa daga Afirka za su shiga kasuwannin Amirka cikin sauki
- sai shirin da shugaba Obama ya kirkira na kulla wata hanya da za ta hada miliyoyin ‘yan nahiyar domin ci gaba
Sai dai nasarar da ake fatan gani a shirye-shiryen na tafiyar hawainiya.
Afirka na da kashi daya ne cikin 100 na kasuwancin kasashen duniya na Amurka, wanda fitar da man fetur daga Najeriya da Angola ya mamaye.
Mista Blinken ya bayyana irin damar da haɗin kai zai samar.
“A matsayinmu na ƙasa mafi girman tattalin arziki a duniya da kuma nahiyar da tattalin arzikinta ke haɓaka,” akwai yiwuwar “mu iya gina wata alaƙa ta tattalin arziki mafi girma a ƙarni na 2021”.
Don taimakawa, ya sanar da aniyar ƙasarsa ta tura wakilin zuba jari zuwa sakatariyar gamayyar kasuwanci ba tare da shinge ba ta Afirka, wadda Tarayyar Afirka ta ƙirƙira don sauƙaƙa harkokin kasuwanci da kuma kyautata rayuwa a yankin.
Asalin hoton, AFP
“Shugaban Senegal kuma shugaban Tarayyar Afirka na yanzu, Macky Sall, ya ce “Afirka na son gina alaƙa da Amurka mai ƙarfi” a jawabinsa
A bayyane take cewa Amurka na duba hanyoyin ƙulla harkokin tattalin arziki.
Baya ga girman tattalin arziki da Afirka ke da shi, ita ce ke da al’umma ta matasa mafi yawa a duniya.
Hakan na nufin masu sayen kaya na ƙaruwa kamar yadda masu neman aikin yi ke ƙaruwa – abubuwan biyu na ƙara wa kasuwanci a yankin armashi.
Sai dai kuma akwai barazanar tsaro da hakan ke haifarwa.
Idan tattalin arziki bai haɓaka ba, akwai yiwuwar matasa su ɗunguma neman kuɗi ta hanya mafi hatsari.
Hakan ya jawo rikice-rikice a Kusurwar Afirka da kuma yankin Sahel da ke Afirka ta Yamma.
Akwai hannun Amurka a yunƙurin daƙile rikicin a yankunan biyu, inda take aikin haɗin gwiwa da gwamnatocin ƙasashen.
Sai dai kuma ɓullar ƙungiyar mayaƙa ta ƙasar Rasha mai suna Wagner a ƙasashen Afirka da dama ta jawo alaƙa tsakanin ƙasashen da Amurka ta yi tsami, har ma da sauran ƙasashen Turai.
Akwai wasu ƙasashen na Afirka da dama da ke da alaƙa mai kyau da Rasha. Aƙalla 17 ne daga cikinsu suka ƙaurace wa ƙuri’ar Majalisar Ɗinkin Duniya don yin wadarai da yaƙin da Rashar ta ƙaddamar a Ukraine.
Da yawansu sun ce ba ruwansu amma Amurka ta sha ba su shawarar cewa wannan ba lokacin da ƙasashe za su ce ba ruwansu ba ne.
Ba a ji wani abu mai kama da haka ba yayin taron.
Hakan ba ya nufin Amurka ta daina ƙoƙarin kare haƙƙin dimokuraɗiyya ko kuma na ɗan Adam.
China da Rasha ba sa saka wasu sharuɗɗa wajen yin hulɗa, abin da kan sa wasu shugabannin na Afirka sakewa da su don kar a dinga bibiyar harkokin mulkinsu.
Yanzu da Amurka ta sake jaddada alaƙar, shugabannin Afirka za su duba ko za su iya ci gaba da alaƙar da kuma yadda za su kare manufofinsu.