
Asalin hoton, Getty Images
Tawagar Italiya za ta kara da ta Ingila a wasan neman gurbin shiga gasar nahiyar Turai ranar Alhamis a filin wasa na Diego Maradona.
Tawagogin sun fafata a kakar nan, inda suka tashi 0-0 ranar 11 ga watan Yunin 2022 a Wembley a karawar Nations League.
A wasa na biyu kuwa ranar 23 ga watan Satumabar 2022, Italiya ce ta ci 1-0 a dai Nations League.
Tun kan nan Italiya ta doke Ingila ta lashe kofin nahiyar Turai a Wembley a bugun fenariti, bayan da suka tashi 1-1.
Harry Kane na fatan zama kan gaba a yawan cin kwallaye a tawagar Ingila, zai haura Wayne Rooney.
Kane, wanda kawo yanzu ya ci wa Ingila kwallo 53, kenan ya yi kan-kan-kan da Rooney.
Wannan shine wasan farko da Ingila za ta buga tun bayan gasar kofin duniya, wadda Faransa ta fitar da Ingila a quarter finals.
Ita kuwa Italiya ba ta je wasannin da aka yi Qatar ba, bayan da ta kasa samun gurbi.
Wadanda ke kan gaba a ci wa tawagar Ingila kwallaye:
- Wayne Rooney wasa 120 da cin kwallo 53
- Harry Kane wasa 80 da cin kwallo 53
- Sir Bobby Charlton wasa 106 da cin kwallo 49
- Gary Lineker wasa 80 da cin kwallo 48
- Jimmy Greaves wasa 57 da cin kwallo 44
Ingila za ta buga wasan ba tare da Marcus Rashford da mai tsaron raga, Nick Pope da kuma Mason Mount, wadanda ke jinya.
An dauki matakan tsaro, bayan da aka dage wasan sada zumunta tsakanin Italiya da Ingila tun can baya, saboda kada a ci karo da cikas.
A makon jiya an tsare magoya baya takwas, bayan rikici da ya barke har da kunna abubuwan tartsatsi tsakanin magoya bayan Eintracht Frankfurt da Napoli tun kan wasan Champions League.
Asalin hoton, Getty Images
Gianluca Vialli da kuma Roberto Mancini
Italiya za ta sako wani sako kan Gianluca Vialli a rigar da za su saka, mamba a koci Roberto Mancini, wanda ya mutu a watan Janairu yana da shekara 58 da haihuwa.
Mancini ya ce karawar za ta yi zafi ganin sun saba haduwa a fafatawar ta hamayya.