
Asalin hoton, Getty Images
Manchester United ta karbi bakuncin Fulham a wasan quarter final a FA Cup ranar Lahadi a Old Trafford.
United ta kawo wannan matakin, bayan da ta ci West Ham United 3-1 ranar 1 ga watan Maris a Old Trafford.
Ita kuwa Fulham ta yi nasarar cin Leeds United 2-1 ranar 28 ga watan Fabrairu a wasan zagaye na biyar a FA Cup na bana.
United ce ta biyu a yawan daukar FA Cup mai 12, idan ka cire Arsenal mai 14 jimilla, wadda Manchester City ta fitar da ita a gasar bana.
Ita kuwa Fulham ba ta taba lashe kofin FA Cup ba a tarihi.
United ta ci Fulam 2-1 a gasar Premier League ta bana da suka kara a Craven Cottage ranar 13 ga watan Satumbar 2022.
Tuni dai kungiyar Old Trafford ta lashe Carabao Cup a bana, bayan doke Newcastle United a Wembley.
Kofin farko da ta dauka kenan tun 2017, sannan ta kai quarter finals a Europa League, za kuma ta fusaknci Sevilla gida da waje.
To sai dai United ta dan samu koma baya a wasannin Premier League, musamman doke ta 7-0 da Liverpool ta yi, sannan ta tashi 0-0 da Southampton.
Sai dai duk da haka United tana ta uku a teburin Premier League, ita kuwa Fulham tana ta tara da maki 39.
Babbar kungiya da ke cikin wasannin FA Cup kawo yyanzu har da Manchester City, wadda ta kai daf da karshe, bayan da ta caskara Burnley 6-0 a Etihad ranar Asabar.
Wannan shine karon farko da Fulham za ta buga daf da na kusa da na karshe a FA Cup tun bayan 2010.
Wasannin da za a fafata ranar Lahadi:
- Sheffield United da Blackburn Rovers
- Brighton & Hove Albion da Grimsby Town
- Manchester United da Fulham