
Felix Pangibitan manomi ne da ya wallafa bidiyon shinkafar da ya noma a shafukin intanet
Felix Pangibitan ya sanya hannunsa cikin dan abin da ya yi masa saura a shinkafar da ya noma.
Kusan kashi uku na abin da ya noma sun rankwafa, wasu sun fadi, wasu kuma sun karye sakamakon mummunar guguwar da ta afkawa gonar mai karfin tafiyar kilomita 241 cikin sa’a guda.
”Lamarin da tausayawa,” in ji shi a wani bidiyo da ya wallafa a shafin intanet da ya karade shafukan sada zumunta a Philippines.
”Wannan asara ce, mu na shan wuya kafin mu zama manoma ga kuma abin da ya same mu”.
Babbar asara ce ga Felix da ma kasar baki daya, za a samu karancin abinci, musamman yadda farashin kayan abincin sukai tashin gwauron zabbi a bana.
Gonarsa da ke Nueva Ecija da ke tsuburin Luzon na daya daga cikin dubban gonakin da kakkarfar guguguwa ta afkawa da akai wa lakabi da ”Kwanon shinkafa.” An yi asarar amfanin gona na sama da dala miliyan 22 cikin kwana guda.
”Ba zan iya tuna sunayen guguwowin da suka fadawa kasarmu ba, amma wannan ita ce mafi muni da muka taba gani a rayuwarmu,” in ji shi.
Dan takaitaccen bidiyon da ya dauka mai sosa zukata ya karade kasar, musamman yankunan matalauta da su ma guguwar ta raba da amfanin gonarsu.
Kamar sauran kasashen duniya, farashin kayan abinci, da man fetur, da takin zamani sun yi matukar tashi tun bayan mamayar Ukraine da Rasha ta yi a watan Junairu.
Sai dai lamarin ya munana a Philippines. Dole su ke shigo kayan abinci daga ketare ciki har da shinkafa, da abinci nau’in hatsi kamar Alkama, domin ciyar da tarin jama’ar da suke kasar a lamarin da ya nuna a zahiri ta na cikin gagarumar matsala a yankin Asiya.
Manoman Philippines na shuga shinkafa amma yawanci sai dai a fitar da ita ketare
Kamar yadda Felix zai yi shaida, hatta abincin da kasar ke shukawa ibtila’in ya shafe su, hatta kayan abincin da kasar ke samarwa lamarin ya shafe su.
Yawaitar guguwar da ake fama da ita a kasar, ta daidaita tsuburin baki daya. Philppines ta fuskanci guguwa 16 cikin shekara guda ta kuma daidaita amfanin gona da asarar dukiya mai tarin yawa.
An yi kiyasin guguwar ta janyo asarar amfanin gona da gonakin kansu na dala miliyan 225, kamar yadda ma’aikatar noma ta kasar ta bayyana.
Kasar na bukatar manoma su taya ta ciyar da su, amma tuni su ma manoman ke fadi tashin ciyar da iyalansu. Sama da mutane miliyan biyu da suka dogara da noma wajen ciyar da iyali, yawancinsu matalauta ne.
“Halin da muke ciki ya munana, mu na shan bakar wuya,” in ji Felix , da ya shafe shekaru 30 ya na noma.
“Farashin kayayyaki ya yi tashin gwauron zabbi, haka takin zamani da man fetur. A bangare guda kuma farashin amfanin gona nan yadda suke sama da shekaru goma ba gaba, ba baya. Hakan na nufin abin da muka girbe ba shi da wani amfani.”
Shugaban kasar Philippines Ferdinand “Bongbong” Marcos Jr h ya nada kan shi ministan noma, ya kuma yi alkawarin tallafawa kasar fitowa daga halin da ta ke da inganta noma. Sai dai shi da kan shi ya amince tashin farashin kayayyaki ya kai makura da an gaza shawo kan shi, sakamakon tashin farashin kayan abinci.
A watan Nuwamba, tashin farashin da aka gani da kashi 8 ba ataba ganin shi ba tun watan Nuwambar 2008 da aka fuskanci tashin farashin da kashi 9 da digo 1, lamarin da ya girgiza iyalan kasar.
Mary Ann Escarda, mai shekara 41 na karade birnin Manila a kowacce rana inda ta ke tura kurar da ke dauke da kayan abincin da ta ke saidawa.
Mary na samun kusan dala hudu ne a rana. Tana sayar da Pandesal, wani abincin karin kumallo a Philippines, amma farashin yin shi ya tashi
Duk da mijinta na daukar albashi, amma ba ya isarsu ciyar da ‘ya’ya hudu da Allah ya ba su.
“Domin alkinta kayan abincimu, dole ta sanya na koyawa yara tsarin cin abinci. A baya mu na cin abinci sau uku a rana, amma yanzu daga abincin rana sai na dare muke ci.” in ji Mary a daidai lokacin da ta bai wa daya daga ciki ‘ya’yanta madarar da ta rage musu.
Ta na zaune gida daya tare da iyalanta su 17, domin rage kashe kudi, ta na kuma cikin tsaka mai wuya. Farashin kayan hada Pandecal da ta ke saidawa ya karu.
”Ba zan iya kara farashin abin da na ke saidawa ba, saboda abokan huldata ba za su iya siya ba, lamarin ya tsananta, ba za su kara siya a waje na ba.”
An samu karuwar masu fama da karancin abinci mai gina jiki a Philippines, kamar yadda shirin samar da abinci ta MDD ta bayyana, mutane ba sa iya cin abincin da zai inganta musu lafiya kuma wannan na cikin rashon shekarar 2022 da aka fitar.
Yara da yawa a kasar na fama da lalurar rashin girma, saboda rashin abinci mai gi na jiki
“Mun kasance mutane masu hakuri,” in ji Fermin Adriano, tsohon mai bai wa ma’aikatar harkar noma shawara.
”Duk runtsi mu na iya jurewa. Amma komai na iya sauyawa idan muka gagara sayan shinkafa saboda tsadarta. Mutane ba za su iya cin abinci ba kenan, lallai yunwa za ta kassara su.
”Za mu iya rayuwa ba tare da sikari ba, ko naman alade, ko farar albasa. Amma rayuwa ba za ta yiwu babu shinkafa ba, saboda ita ce dai abicin da kowa ke ci ya kushi. Idan hakan ta faru to bala’in gaske ya fara kenan.”
”Ga matalauta kuwa, rashin wadatar abincin ya dade da girgiza iyalai, musamman matasa.”
Alamun halin da kasar ke ciki ya bayyana karara lokacin bukukuwan Kirsimati, inda fitilu kalilan aka kunna a titunan Manila.
Lokacin hutu ne gagarumi a duk shekara, ana fara bukukuwan tun daga watan Satumba sakamakon hutun da ake farawa daga lokacin har sai bayan sabuwar shekara.
Za a fi gane komai a bayyane daga watannin farko na sabuwar shekara. Shugaba Marcos ya amince da tsawaita dokar rage farashin kayan abinci da rage harajin kayan da aka shigo da su zuwa karshen shekarar 2023.
Ya kuma yi bayani kan farkin da ya ke da shi na wayar gari ana saida kilo daya na shinkafa kan Pesos 20 na kasar, wata kasa da dala daya ta Amirka.
Tallafi ka iya sassauta lamarin na dan lokaci, amma a bayyane ta ke Philippines wata rana za ta iya noma abin da daukacin kasar za su amfana da shi, amma ta na bukatar karin manoma da amfani da sabbin dabarun zamani domin tabbatar da hakan.
”A tunanin ku, za mu so nan gaba ‘ya’yanmu su yi noma, alhalin ba mu tsinci komai a ciki ba?” in ji Felix.
”Gaskiya ana bukatar gagarumin sauyi. ‘Yan siyasa na kunfar bakin su na son inganta fannin noma, idan da gaske suke, mu gani a kasa domin babu alamun da suka nuna hakan.”