
Asalin hoton, BOBBY BOSTIC
A lokacin da aka sako Bobby Bostic daga gidan yari a watan Nuwamba, bayan ya yi shekara 27 a cikin shekara 241 da aka yanke masa, abubuwa da dama sun zame masa sabbabi.
Kama daga wayar salula (“Me ya sa mutane suke sambatu su kaɗai?”) zuwa mutane suna magana da sifikarsu (“Kamar na ce wanne sabon abu ne haka?”).
Ga na’urorin da suke bai wa mutum abin sha (“Ka kaɗa hannu sai ruwa kawai ya fito?”)
Lallai duniya ta sauya ba ɗan kaɗan ba, idan aka kwatanta da watan Disamban 1995.
Sai dai babban abin da ya fi zame masa baƙo, shi ne mutanen.
“Yadda suke da fara’a, idan an kwatanta da gidan yari,” kamar yadda mutumin mai shekara 44 ya bayyana.
“Idan ka shiga shagon sayayyar kayan abinci, sai ka ji ana ce maka `Ranka ya daɗe, kana buƙatar taimako ne?` A gidan yari kuwa, ba wani abin arziƙi sai murtuke fuska da cin zarafi…”
Har yanzu yana ƙoƙarin daidaita yadda yake jin mutane suna magana.
“Ya kake, lafiya dai ko?” maimakon “Kada ka matso kusa da ni,”
“A nan waje kuwa, abubuwa ne na alheri. Mutane suna ta murmushi abin su.
Ƙananan yara suna ta ɗaga ma hannu. Wannan ai ita ce rayuwa. Wannan ne daidai. Haka ya kamata rayuwa ta kasance.”
Ina tunanin zai yi wuya mutum ya saba, bayan shekara 27 yana cikin ƙangi na rashin mutunta mutum…
“A`a, saboda a can cikin zuciyarka, kana son mutuntawa. Kana son waccan musabahar ta mutuntawa… ita ce rayuwa.
Shi ne abu mai kyau. Shi ne farin cikin zama ɗan’adam.”
Dare 10,000 a garƙame
Bayan kwashe kusan dare 10,000 a kulle, ranar 8 ga watan Nuwamba, 2022 ce ta ƙarshe ga Bostic. Sai dai ya kasa tsaye ya kasa zaune saboda ɗokin shaƙar iskar ‘yanci.
Maimakon haka, ya kwashe tsawon daren yana shirin barin ɗan ɗakin nasa na kurkuku.
Ya bar wa sauran fursunonin abubuwan da ya mallaka, in ban da abu ɗaya. Keken rubutunsa da ke ɗauke da abubuwa masu yawa na tarihi.
-labarai masu yawan gaske – da zai bari a baya.
Da hasken rana, riƙe da kayansa da ya kwaso daga ɗakinsa na kurkuku, ya duba allon da ke ɗauke da sunayen fursunoni, ya ga an rubuta kalmar an sake shi a gaban sunansa.
Ya ce “Ban ɗauka da gaske ba ne, sai da na ga kalmomin.
“Da na gani, sai na ji kamar an tsunduma ni a aljanna.” Yanzu fitarsa ta tabbata, Bostic ya sa kayansa na tafiya gida. Bayan ya kwashe shekara 27 cikin kakin fursuna mai launin toka-toka, ya zaɓi tufafi ƙyalle uku mai ruwan bula.
“Tana nuna shiga sabon babi a rayuwata,” in ji shi.
“Sabuwar mu’amala ta rayuwa.” Shekara 25 baya, Mai shari’a Evelyn Baker ta sanar da Bostic cewa za a tsare har sai ya “mutu a sashen gyara hali”. Amma a yanzu, da ƙarfe 7:30 na safiyar watan Nuwamba, Bobby ya fice daga gidan yari a matsayin mutum mai ‘yanci, rigar da ya sa, da murmushinsa sun cika wurin da haske da annuri.
Wata mace sanye da wata baƙar hula ta matsa gaba don rungumar sa.
Garin yaya aka haihu a ragaya?
Tafiyar da ta zo ƙarshe cikin runguma a wajen gidan yari, ta faro ne a watan Disamban 1995, wata rana mai tsawo da ke cike da afa miyagun ƙwayoyi a Durban cikin St Louis.
Bayan shan barasa, da zuƙar muguwar ciyawa da sauran kayan maye, Bostic ɗan shekara 16 da abokinsa Donald Hutson sun tafi yin fashi da makami.
Suka yi wa wata ƙungiya da ke bai wa mabuƙata kyautukan kirsimeti sata. Suka yi harbi da bindiga (an yi sa’a, ba su ji wa kowa rauni ba). Suka yi amfani da bindiga suka ƙwace wa wata mata mota.
Aka yi wa Bostic tayin idan ya amsa laifinsa, za a yi masa sassauci ciki har da ɗaurin shekara 30, amma ya yi watsi da tayin.
Kotu kuwa ta same shi da laifi. Mai shari’a Baker ta yanke masa hukuncin ɗauri, saboda laifuka guda 17 da aka same shi da aikatawa, ya zama zai yi shekara 241 a matsayin fursuna.
Shi kuwa Hutson ya amsa tayin, ya yarda ya aikata, aka yanke masa ɗaurin shekara 30.
Kyakkyawan fata bayan hira da BBC
Da BBC ta soma zantawa da Bostic a 2018, ya fara tunanin akwai kyakkyawan fata.
A 2010, Kotun Ƙolin Amurka ta yanke hukuncin cewa bai kamata ƙaananan yaran da shekarunsu ba su kai balaga ba, a dinga yanke musu hukunci ɗaurin rai-da-rai, ba tare da yi musu sassauci a laifukan da ba na kisan kai ba.
A 2016, aka ce ya kamata wannan sabon hukunci ya haɗa har da hukunce-hukuncen da aka yi a can baya, kamar irin na Bostic.
Sai dai, jihar Missouri ba ta son sakin Bostic.
Ta ce ai ba daurin rai-da-rai aka yanke masa ba – hukunci ne daban-daban na laifuka iri daban-daban da aka yi su lokaci ɗaya.
In ji ta, ya samu damar samun sassauci a “ƙarshen shekarun tsufa”.
A watan Afrilu na 2018, wata guda da BBC ta zanta da shi, Kotun Ƙolin Amurka ta yi watsi da ƙarar da Bostic ya ɗaukaka. Ba ta faɗi dalili ba.
“Yawancin mutane a wannan lokaci sun haƙura,” Bostic yake bayani. “Ana hana ka, babu abin da ya rage.”
Sai dai Bostic bai haƙura ba.
Ya koma cikin littafansa da suke taimaka masa – Ya fi son Napoleon Hill (Tudun Napoleon) – ya koma kan keken rubutunsa.
Ya ci gaba da buri, wasiƙa ɗaya bayan daya.
Asalin hoton, ACLU
Gyara ne a sabuwar dokar Missouri da ke tayin sassaucin shekaru a gidan yari ga waɗanda tun suna yara, aka yanke musu hukuncin ɗaurin shekaru masu yawa, gyaran da ya sake bai wa Bostic wata damar.
14 ga watan Mayu, 2021 – rana ta ƙarshe ta zaman yin doka a Missouri – ba a dai amince da wannan doka ba.
“Ban wani sa rai sosai ba,” in ji Bostic.“Yawanci, idan ba a amince da doka a watan Janairu ko na Fabrairu ba, babu wata dama ta samun nasara.”
Daga nan sai Bostic ya samu wani saƙo daga wani da suka saba musayar saƙo a rubuce.
“Gidan yari ya fara bari muna samun saƙonni ta imel” in ji Bostic.
“Wani ya aiko min da wani rubutu da aka yi a jaridar Missouri, yana sanar da ni cewa an amince da dokar… ikon Allah. Sai ina ji kamar mafarki ko tatsuniya.
Anya gwamna zai sa hannu a kan dokar kuwa?”
Ai kuwa Gwamna Mike Parson ya sa hannu. Godiya ga “Dokar Bobby”, Bostic – da sauran ɗaruruwa – sun cancanci samun afuwa.
An sa ranar sauraren Bostic a watan Nuwamban 2021.
“Sai dai ban san me zai auku ba,” ya bayyana. “Ƙa’idojin sakin mutum daga gidan yari, ba masu sauƙi ba ne”.
A zaman sauraren ƙorafe-ƙorafe, an bai wa fursunoni damar samun wakilcin mutum ɗaya don ya taimaka musu.
Bostic ya san wa zai tuntuɓa – mai shari`ar da ta ce masa a kurkuku zai gama rayuwa.
Ta inda aka hau, ta nan ake sauka
Ma shari’a Baker – wadda, a 1983 ta zama mace baƙar fata ta farko da aka naɗa matsayin mai shari’a a Missouri – ta fara tambaya a kan hukuncin Bostic a wajen shekara ta 2010.
Shekara biyu bayan ta yi ritaya, a lokacin da take karanta bambancin tunani tsakanin ƙwaƙwalwar yara da ta manya.
A shekara 25 da ta yi tana aikin shari’a, shi ne hukuncin da ta taɓa yi, amma ta zo ta yi nadama.
A watan Fabrairu na 2018, ta yi wani rubutu a jaridar Washinton Post, tana kiran hukuncin da aka yi wa Bostic a matsayin “rashin tausayi da rashin adalci”.
Bayan wata ɗaya ne ta zanta da BBC tana maimaita wannan saƙo.
Saboda haka, me ta ce a wurin sauraron ƙorafe-ƙorafen neman sassaucin?
“Bobby yaro ne ɗan shekara 16 wanda na yi masa hukunci daidai da babban mutum baligi, hakan kuwa ba daidai ba ne,” ta sanar da BBC yanzu.
“Na zauna tare da Bobby da ‘yar uwarsa. Na ga yadda ya canza daga ƙaramin yaro mai cike da laifukan ƙuruciya, ya girma ya zama mai matuƙar tunani da kula.”
Bobby ya samu ‘yanci
Kamar Mai shari’a Baker, ɗaya daga cikin waɗanda Bostic ya yi wa laifi a 1995 ya yi rubutu don nuna goyon baya kan batun (BBC ta tuntuɓi wasu daga cikin waɗanda Bostic da Hutson suka yi wa laifi, sai dai babu wanda yake so ya fito bainar jama’a ya yi magana).
Da taimakon su batun sassaucin ya kai ga nasara.
“Da zan iya ƙafafuwan amalanke, da na yi, “ in ji Mai shari’a Baker.
Shekara ɗaya bayan sauraren afuwar, wanda ta runguma a wannan hantsi na watan Nuwamba, mutum ne mai `yanci.
“Kamar rana ce ta Kirsimeti da Sabuwar Shekara aka haɗe duka a wuri ɗaya,” in ji ta.
“Na fara kuka. Bobby ya samu ‘yanci.”
Bayan haɗuwa da Mai shari’a Baker da abokai da dangi da magoya baya, Bostic ya tafi cin abincinsa na farko a wajen gidan yari, rabon da ya ci abinci irinsa tun 1995.
Shekara 24 ana cin ganyayyaki, ya zaɓi abinci dangin alkama da masara, a da hakan ba zai yiwuwa ba.
“Na shiga cikin mota na janyo duk abincina,” kamar yadda ya yi bayani.
“Idan ka fito daga kurkuku, ka bi titin da ka shekara 27, ba ka bi ba. Akwai wannan abin da ake kira zazzaɓin motsawa.”
Bayan ya gama farfaɗowa, ya tafi gidan ‘yar’uwarsa da ke yankin kudu na St Louis, birnin da a cikinsa ya girma.
Ya ce a ranar fiye da mutum 400 ne suka zo gaishe shi.
“Sun yi jerin-gwano a kusa da gidan,” in ji shi. “Idan na juya nan, sai in yi musabaha da wannan, wannan ɗan kawuna ne, wannan gwaggona ce, wannan kawuna ne, wannan abokina ne… na kai har ƙarfe 2 na safiya.”
Bidiri ne na duniya da za a iya cewa ba shi da ƙarshe.
Sadaukar da kai ga ayyukan agaji
Bobby da ‘yar’uwarsa suna gudanar da aikin ba da agaji, a ƙarƙashin gidaniyar Dear Mama.
Da yake ba da tallafin abinci, da kayan wasan yara, da sauran tallafi ga iyalai masu ƙaramin ƙarfi a St Louis (An sa sunan mahaifiyarsa da ta riga mu gidan gaskiya Diana wadda Bobby ya ce, ‘ta yi wa mutane masu yawan gaske alheri, duk da mu kanmu ba a wadace muke ba”).
Yana gudanar da wani taro na ƙara wa juna sani a kan rubuce-rubuce duk ranar Asabar a cibiyar tsare kangararrun yara ta birnin, da fatan zai ci gaba da wannan ƙoƙari.
Sai dai kamar aikin ba da agajin, shi ma wannan, aiki ne na sa-kai.
Yana samun kuɗaɗensa ne daga littattafan da yake sayarwa- akwai guda bakwai a shagon intanet na Amazon, duka ya rubuta su ta hanyar amfani da keken rubutunsa.
Daga nan ya kama hayar gida mai ɗaki ɗaya, yana biyan kuɗin haya.
Burin ƙara gina rayuwa
Yana fatan samun cikakken aiki don ba da gudunmawa ga ci gaban al’umma, ko na tallafa wa matasa, da sauransu.
Duk da haka – ko da kuɗi suna wahalar samu – mamaki ko godiyarsa ba za su dusashe ba, ga iskar ‘yanci da yake shaƙa.
“Har yanzu ina fama da wasu ‘yan ɗaiɗaikun matsaloli,” in ji shi.
“Amma in ba wannan ba, rayuwa a nan waje tana da daɗi, a kullum.
Idan duba firji, zan ga abubuwa birjik a ciki sai wanda na zaɓa. Idan shiga babban bahon wanka – tsawon shekara 27 kenan ban yi wanka a irinsa ba! Ba na sakaci da komai”.
Bostic yana da wata dama ta gudanar da rayuwa, kuma yana godiya da hakan. Sai dai tsohon abokinsa na tun a watan Disamban 1995, ba shi da ita.
Donald Hutson – wanda ya amince da tayin sassauci kafin yanke masa hukuncin shekara 30 – ya mutu a watan Satumban 2018.
Rahoton wani bincike ya nuna cewa ƙwayoyin magani masu yawan gaske, da suka saɓa wa ƙa’ida da ya afa ne, suka zama ajalinsa.
Ya cancanci sassauci a watanni tara da suka biyo baya.