
Asalin hoton, EPA
Hukumomi a Pakistan na bincike kan yadda wani ɗan ƙunar bakin wake ya kutsa cikin masallaci a birnin Peshawar mai cike da tsaro tare da tayar da bam ɗin da ya kashe mutane akalla 100.
Harin wanda yana ɗaya daga cikin hare-hare mafi muni da ƙasar ta fuskanta, ya kaɗa ‘yan Pakistan. Yawancin waɗanda suka mutu jami’an tsaro ne da suka je yin sallah.
‘Yan sandan ƙasar waɗanda ke kan gaba a yaƙi da mayaka suna da yaƙinin cewa an kai harin ne da nufin karya musu gwiwa.
Wannan na zuwa ne watanni biyu bayan da kungiyar ‘yan tawaye ta sanar da tsagaita buɗe wuta. Tun bayan nan, an ci gaba da samun ƙaruwar tashin hankali, inda ake kai hare-hare a-kai-a-kai kan ‘yan sanda da sojoji.
Da farko an zargi kungiyar masu iƙirarin jihadi ta TTP da kai harin na bam a ranar Litinin, abu kuma da kungiyar ta musanta, da ɗora shi kan kwamandan kungiyar da ya bangare.
Sai dai masu lura na aza ayar tambaya kan musanta kai harin da kungiyar ta yi – sun ce hakan wani yunkuri ne na raba hankali.
A baya, kungiyar ta TTP ta daina kai hari kan masallatai da makarantu da kuma kasuwanni, inda ta koma yaƙi gadan-gadan da jami’an tsaro ba kan mutanen Paistan ba.
Asalin hoton, .
Kungiyar TTP ta ɗauki tsawon shekaru tana yaƙi da sojoji da kuma ‘yan sandan Pakistan, abin da ya janyo mutuwar mutane da dama. Kungiyar na da aƙida ɗaya da kungiyar ‘yan tawaye ta Taliban, amma basu da wata alaƙa.
Cikin manyan buƙatunta, kungiyar na son assasa abin da ta sani kan dokokin Shari’a a arewa maso yammacin Pakistan.
A wani lokaci cikin shekara goma da ya wuce, TTP ta yi barazanar tarwasa Pakistan daga yankunan da take iko da su a kusa da iyaka da Afghanistan mai cike da tsaunuka wanda kuma ya zama matattara ta mayaƙa na gomman shekaru.
Ɗaya daga cikin manyan hare-haren da ta kai wanda aka yi Alla-wadai da shi a duniya ya faru ne a watan Oktoban 2012, lokacin da aka harɓe wata yarinya ‘yar makaranta mai suna Malala Yousafzai. Ta kasance tana kamfe kan ilmantar da ‘ya’ya mata.
Wani samamen sojoji da aka kaddamar a shekaru bayan nan, bayan harin da aka a wata makaranta a brinin Peshawar – kungiyar TTP bata ɗauki alhakin kai harin ba da ya kashe mutum 141 wanda yawanci yara ne – ya yi matukar rage ƙarfin kungiyar a Pakistan.
Bayan fushi da ya shiga zukatan mutane, sojojin sun yi nasarar lalata wuraren mayaƙa da tura su zuwa kan iyaƙa da Afghanistan. An samu raguwar rikice-rikice a Pakistan.
Sai dai a shekarun baya-bayan nan, an samu ƙaruwar hare-haren kungiyar TTP da wasu kungiyoyin mayaƙa a arewa maso yammacin ƙasar.
Bayan da Taliban ta sake karɓar iko da Afghanistan a 2021, tsohon Firaministan ƙasar, Imran Khan, ya yi wa ‘yan tawaye da ke ɓoye a kan iyaƙa tayin dawowa gida don ci gaba da rayuwa – muddin suka ajiye makamansu.
Mayaƙan sun dawo, amma sun ki miƙa makamansu – nan ne kuma matsalar da ake fama da ita ta faro. Wannan kuma ya janyo karyewar tattaunawar da Imran Khan ya fara.
Asalin hoton, EPA
Sabbin shugabannin siyasa da na sojoji da suka zo bayan hamɓarar da firaministan a shekara da ta gabata, sun ki amincewa da buƙatar mayaƙan, inda suka dakatar da magana da ‘yan tawayen.
A sakamakon hakane, TTP ta janye yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta a watan Nuwamba da dawo da kai hare-hare.
Ashraf Ali, mai kungiyar bayar da tallafin jini, ya ce mutane a Pakistan na rayuwa cikin fargaba.
“Ni, tare da iyalina da kuma dukkan ‘yan Pakistan, na cikin tashin hankali. Mutane na cikin tsoro a nan,’’ kamar yadda ya faɗa wa BBC.
“Mutane na cikin damuwa kan abin da zai faru nan gaba saboda tafiya ce mai nisa daga aikin ta’ddanci da yawon buɗe ido a Peshawar, inda yanzu ta’addanci ya yi mummunar tasiri kan birnin.’’
Pakistan ta ce a shirye take ta fuskanci masu iƙirarin jihadin. Sai dai, ‘yan sandan ƙasar basu da isassun kayan aiki na faɗa da ‘yan ta-da-ƙayar-bayan waɗanda ke da manyan makamai.
Hare-haren masu iƙirarin jihadi a baya-bayan nan sun haɗa da far wa ofisoshin ‘yan sanda – a wasu lokuta ‘yan sandan basu ma yi ƙoƙarin tunƙarar maharan ba.
Mutane na son a kawo ƙarshen rikicin, inda a yanzu masana ke kiraye-kirayen gudanar da wani samamen soji don yin galaba kan mayaƙan kamar yadda ya faru a 2014.
Sai dai, ‘yan Pakistan na cikin ɓacin rai na yunkurin ƙasar na yaƙi da ayyukan mayaƙa, wanda ya shafe gomman shekaru ana fama da shi.
Mutane da yawa na da yaƙinin cewa akwai wasu cikin jami’an tsaron ƙasar ta Pakistan da kuma gwamnati waɗanda ke ragawa mayaƙan, kuma wannan shi ne dalilin da ya sa ba a samu damar magance matsalar ba.