Abin da ya kamata ku sani kan ƙirƙirar kazar da za ta dinga haifar kaza zalla



'Yan tsakin da aka jirkita wa ƙwayoyin halitta za su dinga haihuwar kaji ne kawai ban da zakaru

Asalin hoton, Ori Perez/Volcani

Bayanan hoto,

‘Yan tsakin da aka jirkita wa ƙwayoyin halitta za su dinga haihuwar kaji ne kawai ban da zakaru

Masu bincike a Isra’ila sun ce sun ƙirƙiri kazar da aka yi wa ƙwayoyin halittarta kwaskwarima don su dinga haifar kaji mata zalla.

Ci gaban zai iya tseratar da biliyoyin zakaru da ake yankwa a faɗin duniya duk shekara, waɗanda ake ƙararwa saboda ba sa yin ƙwai.

Kajin mata, da kuma ƙwayayen da suke sakawa bayan sun girma, ba sa ɗauke da ƙwayar halittarsu ta asali.

Ƙungiyar kare haƙƙin dabbobi ta Compassion in World Farming ta goyi bayan tsarin.



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like