
Asalin hoton, Getty Images
An kusan rufe kasuwar saye da sayar da ‘yan kwallo a wasu kasahen Turai har da gasar Premier da aka yi hada-hada mai tsako.
Ga jerin wasu batutuwan da ya kamata ku sani kan ranar karshe da za a rufe kasuwar a watan Janairu.
An fara cinikayya daga 1 ga watan Janairun 2023, wadda ake sa ran karkare komai ranar Talata 31 ga watan Janairu a gasar Premier League.
Duk wani sabon dan wasa da za a dauka nan gaba zai iya buga Premier League a makon gaba, amma idan an gabatar da shaidar ciniki kafin wasan gaban.
A Scotland za a rufe kasuwar a tsakar daren 31 ga watan Janairu.
Sauran kasashen Turai za su kammala hada-hada ranar 31 ga watan Janairu, amma da karfe biyar agogon GMT a Bundesliga, karfe bakwai agogon GMT a Serie A da karfje 11 na dare agogon GMT a La Liga da kuma 11:59 agogon GMT a Ligue 1 ta Faransa.
Sama da fam miliyan 437 aka kashe a Premier League wajen cinikayyar ‘yan kwallo a wannan lokacin.
‘Yan wasa shidan da Chelsea ta dauka a Janairun nan ta kashe fam miliyan 181 har da kudin sayenn Mudryk – Leeds ta kafa tarihin sayen dan wasa mafi tsada a tarihinta, bayan daukar Rutter kan fam miliyan 36.
Daukar Gakpo da Liverpool ta yi fam miliyan 35.4 zuwa fam miliyan 44.3 idan ka hada da tsarabe – tsarabe, PSV ta ce shi ne mafi tsada da ta sayar a tarihi.