
Asalin hoton, SPL
Tsutsar ciki dai yanayi ne na yadda tsutsosi ke zama a cikin mutum. Suna yaɗuwa zuwa ƙananan hanji inda suke zama tare da haifar da illoli ga ɗan adam.
Wasu tsusosi na taɓa hantar jikin mutum ko maɗaciya saboda nan ne ruwa ke zama don sarrafa nau’in abinci.
Suna kuma da rukuni daban-daban da gurbin da suke zama a cikin ɗan adam.
Cutar tsutsar ciki bata bar manya da ƙanana ba musamman waɗanda ke yankunan karkara saboda an fi samunta a wuraren da babu tsaftar muhalli.
Me ke janyo ta?
Dakta Tasiu Ibrahim, malami a tsangayar koyar da aikin likita na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, ya ce abin da ke janyo ta ita ce mu’amala da ƙasa wato wuraren da suka gurɓata da bahayar ɗan adam da ke yaɗa kwayayen cutar.
Ya ce tsutsar ciki na da jinsi, inda macen ta ke yin kwayaye 200,000 a kowace rana.
Ya kuma ce yin bahaya a waje na iya janyo cutar saboda idan bahayar ta buce, za ta iya shiga cikin ƙasa, inda mutane kan cire amfanin gona ba tare da sun sani ba wanda kuma zai gurbata abincin.
Malamin ya ci gaba da cewa akwai wani yanayi na idan mutane musamman manoma da yara idan suka taka wurin babu takalmi, za ta iya shiga ta kafafunsu.
Illolin tsutsar ciki
Game da illolin da tsutsar ciki ke haifarwa, Dakta Tasiu Ibrahim ya ce ga yawancin mutane ta kan zauna a cikinsu ba tare da haifar da matsaloli ba.
Ga irin nau’in illolinta kamar haka:
- Ciwon ciki
- Tashin zuciya
- Yawan amai
- Gudawa tare da jini
- Yawan shiga bayi da fitar baya
- Kasala da rashin kuzari
Ya ce babbar illar da take haifar shi ne tsotse jinin mutum.
Ya kuma ce za ta ƙawar da abincin da yara masu tasowa suka, inda za a yaro baya girma wanda kuma zai taɓa walwala da kwakwalwarsa.
Lokacin shan maganinta
Dakta Tasiu Ibrahim ya ce ma’aikatan lafiya na samar da magani daga lokaci zuwa lokaci ga waɗada ke fama da lalurar.
“Yawancin mata masu juna biyu lokacin awo idan aka lura suna rasa jini ana basu irin wannan magani domin ƙawar musu da tsutsar ciki, ana maimaita basu a-kai-a-kai bisa tambayar ko sun sha maganin,’’ in ji Malamin.
Bambanci tsakanin tsutsar ciki da macijin ciki
Malamin ya ce babu bambanci tsakanin lalurorin biyu saboda duk abu ɗaya ne.
Ya ce suna da na’uka daban-daban, akwai kuma ‘yan ƙanana, inda wasu ke tsawo su zama macijin ciki wanda kan girma kamar fensiri da ake rubutu da shi.
Ya ce bambancin da suke da shi kaɗai shi ne nau’in jinsi da rukuninsu da kuma karfin illoli da za su yi wa mutum.