
Asalin hoton, Getty Images
Chelsea za ta karbi bakuncin Fulham a Stamford Bridge ranar Juma’a a gasar Premier League.
Chelsea na jiran jin ko dan wasan da ta dauka a Janairu, Enzo Fernandez zai iya buga mata fafatawa da Fulham, idan FA ta kammala yi masa rijista.
‘Yan wasan Ingila Ben Chilwell da Reece James da Raheem Sterling da kuma Ruben Loftus-Cheek suna da koshin lafiyar buga karawar.
Sai dai Joao Felix ba zai yi wasan ba, sakamakon dakatarwar jan kati da aka yi masa.
Fulham na auna koshin lafiyar Sasa Lukic da kuma Cedric Soares.
Ba wasu ‘yan wasan Marco Silva da suka ji sabbin rauni, in banda Neeskens Kebano.
Karawa tsakanin kungiyoyin biyu
Fulham ta ci Chelsea 2-1 a Craven Cottage ranar 12 ga watan Janairu – watakila ta yi mata gida da waje kuma a karon farko.
Wannan ce kaka ta 38 da suke buga mataki daya a tare.
Wasa biyu kadai Fulham ta ci Chelsea a karawa 37 da ta kai ziyara a lik, shi ne wanda ta yi 2-1 a Maris din 1964 da 2-0 a Oktoban 1979 a rukuni na biyu
Wasa 15 da Chelsea ta yi a gida a baya, Fulham ba ta yi nasara ba, inda Chelsea ta Fulham ci 2-0 a karawa uku baya da suka yi.
Asalin hoton, Getty Images
Chelsea ta yi nasara hudu daga karawa 15 a dukkan fafatawa da canjaras hudu aka doke ta bakwai.
Ba ta yi nasara ba a karawa tara a Premier League a kakar nan da kungiyoyin da ke samanta a teburi ba.
Fulham tana ta bakwai a teburi da tazarar maki biyu tsakaninta da Chelsea ta 10.
Wannan shi ne wasan farko da Chelsea za ta buga ranar Juma’a tun bayan 1-0 da ta yi nasara a West Brom a Mayun 2017.
Chelsea ta yi amfani da ‘yan wasa 29 a Premier League a kakar nan kawo yanzu, kamar yadda Nottingham Forest da Wolves suka yi.
Graham Potter bai ci wasa ba a karawa hudu a Premier League da Fulham, wanda ya yi rashin nasara biyu da canjaras biyu.
Asalin hoton, Getty Images
Saura wasa daya Fulham ta yi kan-kan-kan da tarihin da ta kafa na cin karawa biyar a waje da ta yi a 2003-04.
Tana kuma fatan cin wasan hanayya na kungiyoyin Landan karo hudu kuma a karon farko a kaka daya.
Wasa shida daga takwas da ta yi rashin nasara da rarar kwallo daya ake doke ta har da karawa hudu baya da ta yi.
A kakar nan Fulham ta samu fenariti tara.
Aleksandar Mitrovic ya ci kwallo a karawa uku a wasan hamayya na kungiyoyin birnin Landan a bana.
Marco Silva bai ci wasa ba a matakin koci da ya ziyarci Chelsea karo hudu.