
Asalin hoton, Getty Images
Leeds United za ta karbi bakuncin Manchester United a wasan mako na 23 a gasar Premier League ranar Lahadi a Elland Road.
Ranar Laraba suka tashi 2-2 a Old Trafford a kwantan wasan mako na takwas a babbar gasar tamaula ta Ingila.
United tana mataki na uku a kan teburi mai maki 43, ita kuwa Leeds mai maki 19 tana ta 17 a kasan teburin kakar bana.
Leeds na auna koshin lafiyar Liam Cooper da Marc Roca da Luis Sinisterra ko za su iya buga mata karawar ta ranar Lahadi.
An sauya Pascal Struijk a minti na 15 da fara tamaula a Old Trafford ranar Laraba, bayan raunin da ya ji, na yin jinya.
‘Yan United da ke jinya sun hada da Anthony Martial da Scott McTominay da kuma Antony.
Watakila nmai tsaron baya, Aaron Wan-Bissaka ya buga wasan bayan rashin lafiya, Casemiro zai yi hutun hukuncin wasa na biyu, bayan jan katin da aka yi masa a karawa da Crystal Palace.
Karawa tsakanin Leeds da Manchester United:
Wasa daya Leeds ta yi nasara a kan Manchester United daga 18 baya a Premier League, shine 1-0 a Elland Road a 2002 da canjaras shida aka doke ta karawa 11.
Watakila Leeds ta yi rashin nasara karo biyu a jere a gida a hannun United a karon farko tun bayan 1976.
Asalin hoton, Getty Images
Mai tsaron bayan Leeds, Pascal Struijk wanda ya ji rauni a minti na 15 a Old Trafford ranar Laraba a wasan da suka tashi 2-2
Watakila Leeds ta yi wasan Premier League na tara ba tare da nasara ba, kamar yadda ta taba yi a 1997.
Wasa biyu kacal ta ci daga 18 baya da ta fafata mai canjaras shida da shan kashi a karawa 10.
Ta barar da maki 15 daga wasan da ya kamata ta lashe a bana, ita ce kan gaba a yawan barar da maki sai Leicester biye da ita a Premier League.
Watakila Wilfried Gnonto ya zama dan wasan da zai ci United gida da waje, bayan Jimmy Floyd Hasselbaink da kuma Mark Viduka.
Crysencio Summerville ya ci kwallo uku ya kuma bayar da daya aka zura a raga a wasa biyar baya a Premier League starts.
Asalin hoton, BBC Sport
Wasa daya Manchester United ta yi nasara daga hudu baya a Premier League da canjaras biyu aka doke ta daya.
Saura karawa daya United ta ci wasa na shida a lik a waje a bana, irin bajintar da ta yi a bara.
Dukkan wasa biyar da ta yi nasara a waje a kakar nan da 1-0 ta yi.
Sai dai United ta yi wasa biyar a jere da kwallaye ke shiga ragarta a Premier League.
Marcus Rashford ya ci kwallo 12 a wasa 14 tun bayan kammala gasar kofin duniya, shi ne kan gaba a wannan kwazon a manyan gasar Turai biyar.
Saura kwallo daya ya rage, Bruno Fernandez ya zura na 100 a raga a Premier League.
David De Gea zai yi wasa na 400 a Premier League, zai zama na farko ba daga Birtaniya ba, mai wannan tarihin.