
Asalin hoton, Getty Images
Liverpool za ta karbi bakuncin Everton a wasan mako na 23 a Premier League karawar hamayya a Anfield.
Kungiyoyin sun kara a cikin watan Satumbar 2022 a Goodison Park, inda suka tashi 0-0.
Liverpool tana mataki na 10 a teburin babbar gasar tamaula ta Ingila mai maki 29, Everton tana ta 18 da maki 18.
Kocin Liverpool, Jurgen Klopp na fatan Diogo Jota ya buga masa wasan na Merseyside Derby, bayan jinyar wata uku.
Wadanda ke jinya sun hada da Roberto Firmino da Virgil van Dijk da kuma Arthur.
Watakila Fabinho ya buga karawar bayan rashin lafiya, amma da kyar Thiago ya buga wasan, yayin da Luis Diaz da Ibrahima Konate ke jinya.
Mai buga wasan gaba a Everton, Dominic Calvert-Lewin na dauke da rauni watakila ya buga wasan in ji Sean Dyche.
Karawa tsakanin kungiyoyin biyu
Wasa daya Everton ta ci a gidan Liverpool a karawa 22 baya a Premier, shine 2-0 a Fabrairun 2021, aka doke ta sau 12 da canjaras tara.
Wasan da suka tashi 0-0 a Satumba a Goodison Park shine canjaras na 12 a tsakaninsu a Premier League.
Asalin hoton, BBC Sport
Liverpool ta kasa cin wasa hudu a Premier League tun da aka shiga 2023 da canjaras daya da shan kashi a uku.
Watakila Liverpool ta yi wasa na hudu ba tare da zura kwallo a raga ba a karon farko tun bayan Janairun 2021.
Jurgen Klopp na fatan cin wasa na 250 a matakin kociyan Liverpool, wanda ya ci karawa 93 da rashin nasara a wasa 71.
Saura wasa daya Klopp ya yi nasara takwas a fafatawar hamayya ta Merseyside derbies, wanda zai yi kan-kan-kan da bajintar Rafael Benitez a kungiyar.
Everton na fatan cin wasa biyu a jere a bana a Premier League, bayan doke Arsenal.
Kungiyar ta yi nasara biyu a wasa 27 baya a manyan karawa, mai canjaras bakwai aka doke ta 18 da cin kwallo daya a fafatawa shida baya a waje.
Watakila Sean Dyche ya zama na hudu a Everton da zai ci wasa biyu a jere da fara karbar aiki a Premier, bayan Joe Royle da David Moyes da Carlo Ancelotti.
Koci biyu ne daga 22 a Everton suka doke Liverpool a wasan farko da suka fuskanci karawar Merseyside a lik, sune Royle a Nuwambar 1994 da Dick Molyneux a Oktoban 1894.
Saura wasa daya Abdoulaye Doucoure ya buga karawa 200 a Premier League.