
Asalin hoton, Getty Images
Liverpool ta ziyarci Manchester City a wasan mako na 29 da za su kara ranar Asabar a Etihad a Premier League.
Da kyar idan dan wasan Manchester City, Erling Haaland zai buga wasan, wanda rauni bai bari ya yi wa Norway tamaula ba.
Haka shima Phil Foden ba zai yi karawar ba, wanda likitoci suka yi wa aiki.
Darwin Nunez zai iya buga wasan, duk da bai yi wa Uruguay tamaula ba, sakamakon rauni.
Luis Diaz wanda ya dade yana jinya ya kusan komawa taka leda, amma ba zai yi wasan da Liverpool za ta kara a Etihad ba.
Thiago da Naby Keita da Calvin Ramsay na ci gaba da jinya.
Kwallo 4-1 da Liverpool ta ci a Etihad ranar 21 ga watan Nuwambar 2015, ita ce nasara daga 13 da ta kai ziyara da canjaras biyar da rashin nasara a bakwai.
Asalin hoton, BBC Sport
Karawa tsakanin Manchester City da Liverpool:
Liverpool na fatan cin Manchester City gida da waje a kakar Premier League a karo na uku, bayan 2005-06 da kuma 2015-16.
Maki 19 City ta bai wa Liverpool tazara – wasa mai tazara da yawa da kungiyoyin za su fafata a karon farko.
City na fatan cin wasa hudu a jere a Premier League a karon farko a kakar nan.
Pep Guardiola ya ci karawa 25 a wasa 27 a gida a lik da kofi da canjaras daya da shan kashi a fafatawa daya.
Tana fatan yin wasa shida ba tare da kwallo ya shiga ragar City ba, ta taba yin hakan tsakanin Nuwamba zuwa Disambar 2020.
Erling Haaland ya ci kwallo 42 a fafatawa 37 a City – Dan wasan da ya ci kwallo da yawa a kaka a lik shine Ruud van Nistelrooy na Man United a 2002-03 mai 44 a raga da kuma Mohamed Salah a kakar 2017-18, wanda shima ya ci 44 a Liverpool.
Kungiyar na turbar watakila ta yi rashin nasara ta uku a jere a dukkan fafatawa ba tare da cin kwallo ba a karon farko tun 2009.
Liverpool ta ci kwallo 13 a waje a kakar nan, amma ta kasa zura kwallo a raga a wasa hudu daga biyar da ta buga a waje.
Idan Liverpool ta yi nasara a karawar, za ta zama ta hudu a Premier League da ta yi nasara 250, bayan Manchester United da Chelsea da kuma Arsenal.
Jurgen Klopp ya doke Pep Guardiola sau 11 daga fafatawa 27, yayin da kociyan City ya yi nasara a wasa tara da canjaras bakwai.
Diogo Jota ya yi karawa 29 bai ci wa Liverpool kwallo ba, tun bayan da ya ci a 2-2 da Manchester City ranar 10 ga watan Afirilun 2022.