A ranar Alhamis ne al’ummar Musulmi suka tashi da azumin watan Ramadana a Najeriya da ma ƙasashe daban-daban na duniya.
Azumi ɗaya ne daga cikin ginshiƙan addinin Musulunci guda biyar – wato shahada, salloli biyar, azumin Ramadana, zakka, da kuma aikin hajji.