
Asalin hoton, Reuters
Girgizar kasa mai karfin maki 7.8 da ta afka wa Syria da Turkiyya a ranar Litinin na iya kasancewa mafi ta’adi a cikin shekaru goma da suka gabata, inda tuni aka sanar da mutuwar fiye da mutum 7,200 a kasashen biyu.
Turkiyya kasa ce da girgizar kasa ta saba afka ma ta. Tsakanin 1939 da 1999, ta fuskanci girgizar kasa fiye da guda biyar.
Tun 1900, fiye da mutum 90,000 sun rasa rayukansu yayin girgizar kasa kimanin 76 da suka auku, kuma rabin wadannan mace-macen tsakanin 1939 zuwa 1999 aka same su.
Wasu iftila’in girgizar kasar da suka auku a cikin shekaru ashirin da suk agabata sun hada da na Haiti a 2021 – wadda ta yi sanadiyyar mutuwar fiye da mutum 2,200 – da na Indonesia a 2018 wadda ta kashe mutum 4,300.
A 2017, fiye da mutum 400 sun mutu a sanadin girgizar kasa.
Ana iya hasashen afkuwar girgizar ƙasa?
Masana kimiyya sun ce ko da akwai yadda za a iya sanin lokaci da girgizar kasa za ta iya afkuwa, babu ani ilimin da zai tabbatar da ainihin lokacin da za ta afku.
To ko ana iya yin hasashen afkuwarta kuwa?
“Abin takaicin shi ne babu yadda za a iya yin haka”, inji Dr Stephen Hicks, masani kimiyyar kasa daga jami’ar Imperial College ta Landan.
“Sai dai abin da za mu iya yi shi ne mu yi hasashe kawai. A wasu wuraren kamar California da ke Amurka da kuma Japan, an fara gano yadda suke afkuwa.
Me ya kamata mutum ya yi domin kaucewa girgizar kasar da ta rutsa da shi?
A zama cikin shirin ko-ta-kwana
Duk da cewa da wuya a iya yin hasashen lokacin da girgizar kasa za ta afku, masana sun bayar da shawara ga mutane su zama cikin shiri.
Cikin abubuwan akwai tanadar abubuwa kamar ruwan sha da tocila da akwatin muhimman magunguna da kuma abincin da ba ya saurin lalacewa.
Kungiyar Red Cross kuma ta ce cikin akwatin da za a tanada, ya dace a samar da kudi da kwafen wasu muhimman takardu kamar na magungunan da likita ya rubuta.
- Mutum ya guji zuwa wani wuri idan wurin da yake ba shi da matsala.
- Da zarar girgizar kasar ta fara, an bukaci mutum ya tsuguna ko ya rika rarrafe, kuma idan akwai wani tebur ko benci, to mutum ya shiga karkashinsa.
- A kauce wa tsayawa kusa da taga ko budadden wuri mai gilashi kamar baranda.
- A fice daga gida ko gini da zarar an sami dama.
- Idan mutum na waje ne to ya kiyaye kusantar wurare kamar gine-gine da wayoyin lantarki da kwalbatoci da inda aka binne bututun iskar gas da na man fetur.
A kiyaye hadurra
Yawancin raunuka na faruwa ne yayin da abubuwan ke fadiwa ko ke tashi daga gidajen suka rufta.
Akwai kuma matsalar iskar gas da ke yoyo daga bututun da ya fashe.
A wasu kasashen akan horra da jama’a yadda ya dace su yi bayan afkuwar girgizar kasa.
Masana na ganin kasar Turkiyya ba ta dauki irin wannan matakin ba, wanda a cewarsu yin haka zai rage yawan mace-mace da raunukan da ake samu a sanadiyyar girgizar kasa.