MANJO HAMZA AL-MUSTAPHA, Tsohon Mai Tsaron Shugaban Kasa, Marigayi Janar Sani Abacha, kuma na hannun damansa. A zantawarsa da tawagar LEADERSHIP HAUSA, Manjo Al-Musatapha ya yi karin haske game da yadda aka kirkiro jihohin nan shida a shekarar 1996, da kuma yadda suka bambanta da saura. Haka zalika ya yi tsokaci kan sha’anin tsaron da ya addabi Nijeriya tsawon shekaru. Ga yadda tattaunawar ta kasance kamar haka:
Ranka ya dade nan da wasu ‘yan kwanaki wasu jihohi kimanin shida a Nijeriya za su yi bikin cika shekaru 20 da kafuwa, wadanda Tsohon Shugaban Kasa, Marigaya Sani Abacha ya kirkira. Shin a matsayinka na makusancinsa wane karin haske za ka yi game da hikimar samar da wadannan jihohi?
To nagode! Na farko, a lokacin da shi marigayi yake kan karaga mutane da dama sun nemi a kirkiro musu jihohi, haka kuma wasu sun nemi a kara musu kananan hukumomi a jihohinsu. Duk da cewa ba zan iya tantance adadin kananan hukumomin a wancan lokaci ba kafin su kai 774 a yanzu, tare da cewa akwai PRC da kuma majalisar koli ta soji, amma duk da haka akwai abubuwan da ya kalla shi da kansa a kowane bangare na Nijeriya. Idan ka dubi tsarin kirkiro wadannan jihohi shida, za ka ga sun bambanta da sauran jihohin baya, wato an yi wani abu sabo wanda ya maida Nijeriya bangarori guda shida wato (Sid Geo-Political Zones). Kuma ya yi haka ne saboda la’akari da yankunan a tarihance. Kowane yanki za ka ga ya bambanta da sauran ta fuskar masarautu, al’ada, dabi’a, zamantakewa da sauransu.
Haka nan kowane yanki akwai takardun bukatar jihohi (Proposals) da yawa, kamar idan ka dauki misali da Gombe, an yi dauki ba dadi ainun kafin jihar ta tabbata, sannan bayan an kirkire ta wasu ba su so a ce Gombe/Gombe ba, amma saboda wasu dalilai Marigayi Abacha ya amince a haka, aka cire Gombe daga Jihar Bauchi. Ka ga ai idan ka dauki Nasarawa za ka ga an kai hedikwata din Lafia, haka Zamfara an kai hedikwata a Gusau. Kuma idan na gaya maka adadin jihohin da al’umma suka rubuto suna son jihohi za ka yi mamaki, amma cikin hikima da kuma bin ka’ida da tantancewa aka amince da wadannan jihohi shida da kuke tambaya a kansu. Ka ga yanzu sun cika shekaru 20 kenan. Kuma tun su din har zuwa yau ba a kara ba.
A dunkule mene ne manufar kirkirar jihohi?
To gaskiya dai a dunkule zan ce muku wadannan jihohi an kirkire su ne bisa cancanta ba alfarma ba, akwai mutane da yawa da zan iya tunawa da muka yi aiki da su a kan wannan fafutika kamar Sarkin Gombe mai rasuwa, irin su Sule Yahya Hamma, Tom Ikimi, Dabid Attah su Aminu Saleh da sauransu da dama, kuma duka wannan a ofishina ake yawan aikin na bayan fage. Wannan kuma saboda yadda kowace al’umma da kungiyoyi suke son a yi nasu kawai, ba sa jiran sai an yi musu, to amma sai marigayi ya ce idan an kasa Nijeriya kashi shida, to kowanne yanki a kara masa daya tak, don kar a bata tsarin cewa mene ne jiha? Kuma me da me ya kamata waje ya zama yana da shi ta fuskar tarihi, yawan jama’a, ma’adanai, al’adu, yawan kananan hukumomi da sauransu.
Kuma marigayi ya sha nanata cewa za mu yi karin jihohi ne bisa cancanta da dacewa kawai ba saboda alfarma da son zuciya ba, wadanda kuma ba su samu ba, to su yi hakuri su kaddara cewa Allah ne Bai nufa ba! Cikin irin wannan fafatiku ina tuna irin manyan sarakunan Nasarawa da ‘yan siyasarsu, haka sarakunan Bayelsa, musamman ma su mutanen Bayelsa da yake shi marigayi ya san yankin sosai saboda ya yi aiki a Fatakwal a matsayin babban mai bada umarnin soji (Brigade Commander), mutane ne da aka dade ana danne su, sun sha wahalhalu da yawan gaske, don haka samar musu jiha da aka fitar da su daga Tsohuwar Jihar Ribas ba karamin ceto ba ne a gare su.
To haka duk takardar da aka kawo shi da kansa yake samun lokaci ya karanta sannan ya dubi yadda wajen yake, domin ya san ko’ina. Haka irin Jihar Ikiti duba da wasu dalilai aka cire su daga Jihar Ogun, domin wannan yankin nan na Ijebu sun ba su matsalar gaske kuma ba a yarda da wannan Jihar Ijebu saboda kamar kabila guda ce kawai, koda yake wasu sun nuna kin amincewa da Ikiti din ma, wai ya za a zabi inda ya fi ko’ina talauci a ba shi jiha, amma akwai da aka yi la’akari da shi a wajen, domin na farko su manoma ne, kuma a tarihance kuma ba a bar su baya ba, wannan ya sanya aka yi la’akari da su.
Sannan kamar Ebonyi a yankin Ibo tamkar karamar hukuma take a wannan wurin, amma saboda a yi adalci, dole aka kutsa aka rage aka kara aka hada suka samu, kuma har yau idan ka duba ai ba su cika shida ba, jihohi biyar ne a yankin amma ya maida su, saboda babu yawan kasa da yawan al’umma da kuma sauran abubuwan da suka kamata a duba. Amma saboda an yi wa sauran, kuma da yake kabilu manya guda uku da kasar nan ke da su, sannan a ware daya ba a kara mata ba, zai jawo fitina, shi yasa aka kutsa aka kirkiri Ebonyi. Sannan idan ka koma yamma, an samar da Zamfara mai hedikwata Gusau ne ba kamar yadda suka so ba, amma sai marigayi ya ce a duba tarihin Usmaniyya tun farko a ga yadda za a kwantar da wannan rigima, domin an riga an cire yankin Kebbi da suke tare da Gwandu, to sai baki ya hadu a kan cewa idan kana so ka samar da zaman lafiya a wannan yankin, to sai ka cire Zamfara da Gusau su ci gashin kansu. Haka nan Nasarawa su ma an dubi tarihi da yawan ma’adinai da kasar noma da yankin ke da shi, sannan da kuma yawan kabilun da suka tattara a wannan waje tun da can, kamar irin mutanen El-Kanemi wanda yaki ya tarwatsa suka watse wasu daga ciki suka sauka a wannan yanki, sannan akwai kuma wasu kabilun Benuwai da Filato da kuma su kansu kananan kabilun wurin tun da farko. Wannan shi ne dalilin da ya sanya aka raba Jihar Filato aka samar da Nasarawa.
A takaice dai duk wanda ya dubi wadannan jihohi guda da Marigayi Janar Sani Abacha ya yi, zai cancanta da dacewa da kum bin ka’idojin da suka kamata har aka samar da su. Haka zalika idan da ka saurari bayanin da ya yi na kirkirar jihoin zaka ji duk ya fadi wadannan abubuwa, ya baiwa wadanda ba su samu ba hakuri, ya nuna cewa ba son rai aka bi ba wajen kirkirar wadannan jihohi. Sannan tsarin da aka bi wajen kirkirar jihohi shi ne aka bi wajen kara kananan hukumomi, domin akwai wadanda aka ciro su daga babbar jihar aka kara su ga wacce aka kirkira din bisa la’akari da abubuwa da dama. Misali kamar yankin nan na Bakasi wacce aka dauke aka cuci kasar nan aka baiwa Kasar Kamaru, wannan cuta ce karara da aka yi wa Nijeriya! Kuma ko ni din nan da zan samu wata dama ko ayau zan sake tada wannan maganar, wannan shine gaskiyar magana, an cucemu haka nan an cuci yaran da za su zo nan gaba.
Kamar mene ne hikimar tayar da wannan batu, ganin cewa kotun duniya ta riga ta mika yankin ga Kasar Kamaru?
Ai zaluntar Nijeriya aka yi! Domin tun marigayi yana da rai, akwai kokarin da aka yi ta yi tsawon lokaci ana tantancewa akan wannan tsauni na Bakasi mai matukar amfani ga Nijeriya, amfaninsa yana da yawan gaske, ba wai don a karawa Nijeriya yawan kasa ba ne a’a, ka ga akwai ma’adinai, man fetir da gas, har ma a cikin ruwan dake wannan wurin akwai abubuwan da Allah Ya dasa masu amfanin gaske! Akwai wadansu kanan kifi wadanda Hausawa ke ce mu su tsutsar ruwa, to duk kasashen Turai na wurin suke ci, shine mafi kyau a duk duniya! Amma ai ka ga mutane da yawa ba su sani ba.
Haka nan akwai irin macijin nan mai suna Mesa, to fatar mesar dake wurin ya bambanta da duk na sauran wurare a duniya. A wasu wuraren akan yi amfani da fatun kada da wasu dabbobin ruwa, amma su wadannan fatun na mesa dake wannan yanki sun fita daban a duniya wajen yin igiyar agogo, takalma, jakunkuna masu tsadar gaske! Wannan dalili ya sa suka yi yarjejeniya da wasu manyan kamfuna na duniya suna basu fatun suna sarrafawa. Wannan wajen yana jawo wa Faransi kudi na fitar hankalin! To ka ga yau mun rasa wurin! Sannan Nijeriya tana cikin kasashen da suke da gabar manyan jiragen ruwa a Afirka, to wannan wajen ya sa muka bambanta ana kiransa Kata-Obam East, Kata-Obam West. Amma son zuciya irin na wasu shugabannin haka suka sadaukar da wannan kokari da binciken da marigayi ya yi ta biya ana tantance mana sai da aka nemi dukkan kasashen da suka mulki Kamaru, aka tattara takardun aka kai su ga hukumomin duniya cewa nan wajen yankin Nijeriya ce, kuma tsawon lokaci duk duniya ta san cewa wannan yanki Kasar Nijeriya ce. Amma bayan tafiyar marigayi wasu bata gari suka bi suka dauke wadannan takardu suka hada baki da wadansu aka kulla karairayi aka ce sune wakilan Nijeriya a kotun duniya, wai shugabannin Nijeriya da kansu suka je suka amince cewa wannan wuri na Kamaru ne, har da kide-kide da murna aka je aka mika wurina haka ya fita a hannunmu.
Kuma fa wancan hukunci ba wai ya tabbata ne babu yadda za a yi ba ne, a’a ko yanzu aka samu jajirtattun shugabanni za su iya kwato wajen, dubi Chana da Japan, haka kuma ga Amurka ga Kanada, ga kuma Ingila ga Pokland, ga Isra’il ga Falasdinu! Duk duniya idan ka duba ire-iren wadannanTsibirai suna nan akwai su, me yasa kotun duniya ba ta iya sasanta wadannan batutuwa ba, ai tana nan.
Ni kaina akwai abubuwa da yawa da na sani game da wannan wuri, kuma duk wasu ne daga cikin binciken da muka yi ta yi tare da Marigayi Abacha! Kuma kar fa ku manta akwai kutungwila da makarkashiya da yawa da aka yi, shine ta yadda suka je suka dauki hayar wasu mutane a hankalin suka rika canza mu su taswirar dake tsakaninmu da Kamaru, har aka wayi wai wajen ya zama na su, alhali shekaru aru-aru an san wajen mallakin Najeriya ne. Kuma kasar nan bata ankara ba har sai da wani bature ya gani, sannan yake shaidawa marigayi Abacha cewa ashe Bakasi din nan bata wurinku yanzu? kuma ni aka fara baiwa wannan takarda sadda baturan suka zo, sannan muka gano ashe akwai hannun wasu munafukai, muka yaki wannan muka yi takardu muka mika ga kotun duniya don shaida. Ka ga irin su Tom Ikime da kuma farfesa Yadudu, wanda shine ma ya yi zarya wajen harhada wadannan takardu, amma duk kokarinsu ya tashi a banza a yau.
Wannan duk nan gaba magana zai taso akansa, tun da yanzu kana magana ne akan kirkiro jihohi, to abinda ya kawo alakar shine, yadda Janar Abacha ya kara inganta wurin nan, domin yankin ya shiga daga cikin yankin kananan hukumomin da ya mayar da su 774 kuma sune dai har zuwa yau. A lokacinsa ya yi kokarin samar da asibitoci, makarantu, bankuna da sauransu, duk don a kara tabbatar wa duniya cewa lallai wannan wuri namu ne mallakinmu ne. kuma da sannu lokaci zai zo da za a sake kwato wannan wuri, domin wadanda suka yi wannan zambar wasunsu suna nan da rai, amma saboda son abin duniya suka sadaukar da wannan waje. Amma kuma da taimakon Allah shugabanni nagari za su shige mana gaba, ai akwai su da yawa.
Ka fito ne daga yankin Arewa maso Gabas, yankin da ya yi ta fama da fitintinu da hare-hare daga Kungiyar Boko Haram fiye da shekaru bakwai da suka gabata. A matsayinka na kwararre a harkar tsaro, ya ya ka kalli wannan jidali da kuma yadda wannan gwamnati ta ke tunkarar lamarin?
To batun Boko Haram wani abu ne mai saukin gaske, amma wasu suka maida shi babban abu, har ta kai yau wannan abu yana baiwa gwamnati wahala! Kuma galibi wasu ne suka ingiza wannan fitina kuma ana kallonsu. Yanzu ma dai tukun mu fara dubawa mu ga wai su wane ne Boko Haram? Me suka son cimma? Yaushe suka fara? Menene dalilin zuwansu? Su wa suka farata? Su wa ke aiko mu su gudumawa? Sannan sai ka dawo ka tambayi cewa su wanene ke aikin rubuce-rubucen kwararru na gidan soja da ‘yan sanda? Sannan wane ne gwamnan yankin? Su wanene shugabannin kananan hukumomin wajen? Su waye sarakunan wajen? Duk a gabansu aka yi ta yin wannan abu, amma an hukunta mutum daya har zuwa yau?
Ai duk kasar da zata tsaya sai abu ya lalace sannan zata fara neman hanyar magance matsalar, to da sauranta, sannan wadanda ya kamata su yi aikinsu suka gaza yi, kuma ba a hukunta su ba, to me kake nema kuma? Ka ga babu adalci anan? Ko kadan ba a yi adalci ba! sMu lokacin muna aiki, na san idan aka ce rikici ya tashi, to farko gwamna ake duba tukun, sannan ma su aikin bada tsaro na wannan jihar, don kowace jiha tana da wadanda hakkin tsaronta ke wuya su, idan dukkan babu wanda ya yi aikinsa, to sun zama ma su laifi. Kuma tun farko idan sun san za a hukunta ba za su fara sakaci ba! Don haka a wannan karon me yasa aka yi wannan shegantaka? Har ya zama akwai masu tsara yadda makamai ke shigowa daga kasashen duniya, akwai masu ba su abinci, kuma su kashe kowa da kowa da suka samu, ka san ba banza ba ne! Kuma wannan magana komai dadewa sai an bincika domin akwai munafurcin wasu daga gida, sannan akwai munafurcin wasu daga waje. Amma dai tambayar da ka yi min shi a takaice wannan gwamnatin ta tadda abu ya rika ya kazamce! Amma ada wasu sun ja wannan rigima saboda abinda suke samu a ciki, wannan tabbas ne. Haka aka kyale wannan barna, ake karkatar da makaman zuwa ga wadanda ake yaka, ake barin wadanda suke yakin don kawai neman tara abin duniya. Kuma a ka’ida duk wanda ya sa hannu a takardar aikin soja, to ya san hakkin dake kansa, kowa ya san huruminsa, hatta babban idan ya taka karami akwai hukunci dake kansa, e, lallai akwai hakkin babba akan kanana akwai hakkin kanana akan babba duk dokar soja akwai wannan, ba wai don kana babba ka rika taka kanana kuma babu komai ba. Kuma wani abin mamaki an bari wasu da ba su san komai a sha’anin tsaro ba, da sunan masun kare hakkin dan Adam, su yi ta shirme suna dalilin lalata abubuwa, idan zai yi aikinsa, to ba a bukatar wani mai kare hakkin dan adam, duka wannan yana kunshe ne cikin soja baki daya, amma idan ana barin wannan kwamacala, kasa tana maida sojojinta ne kamar masu bada hannu ga motoci ne kawai.
Kuma yadda muke gani yanzu da gwamantin take fuskantar su gadan-gadan, ai yawancin wadanda ake kamawa muna gani ba ma ‘yan Nijeriya ba ne! wadanda ma makaman na shigowa ne ta cikin kasashen su, sai a saye su kara so suna tada hankalin, saboda ba su hasara. Amma dubi yadda ada suke yi, a yanka tsofaffi a yanka yara kanana, a yanka musulmi a yanka kirista, a yanka mata a yanka maza, a shiga masallai a kashe mutane a shiga coci a kashe! Ka ga wannan fa ko Fir’auna bai yi haka ba fa! Lallai an bada labarin yadda yake yanka ‘ya’ya da rai, amma alal hakika abinda wadannan mutane suke yi ya wuce nasa. Sannan kuma kar mu manta tsare martabar kasa, dawo da zaman lafiyar kasa aiki ne da ya rataya akan wuyan kowa ba na wani bangare ba.
Koda yake shi shugaban kasa na yanzu ai ya fi kowa sanin wannan yankin na Arewa ta Gabas, ya yi gwamna a wajen, sannan ya yi Babban Kwamnadan Rundunar Soji (GOC) dake Jos kuma shi yake kula da dukkan wancan yankin baki daya. Sannan an yi maitatsine ada, shi ma ba anan ya fara ba? Sannan ai mutanen Chadi sun dade suna aukawa Nijeriya a lokacin yana GOC din, shi ya fatattake su! Janar Buhari ya nuna kwazo ma da sadaukarwa mai yawan gaske don cigaban kasar nan, kuma a lokacin fa da suke wannan gwagwarmayar, kafin ma ka nema taikamon can sama sai ka fara tukun, kuma hakan suka yi, amma da gangan ana so a bata tasiri da darajar soja a Nijeriya.
Ranka ya dade ka yi fice a harkar tsaron Shugaban Kasa. Shin me ya bambanta ka da saura?
To ba na jin cewa ina da wani bambanci a zahiri, kuma bayan da muka gama namu mulkin, ni tsare ni aka yi, don haka ban san irin ayyukan da na bayana suka yi ba! Sai dai kawai abinda na sani shine mun sadaukar da kanmu, duk aikin da ka ba mu, ba za mu je mu bar shi yadda ka bamu ba, sai mun canja shi. Wurin da kake aiki nan ne kuma makarantarka, sannan shine kuma wurin bautarka, domin duk abinda kake yi ka ji cewa al’umma kake taimakawa, zaunar da kasa lafiya, to haka muke tunkarar kowane abu, ba don mu tara kudi ko wani abu ba. Sannan ba ma duba baya, duk wanda zai yi fushi da mu, to ya je ya yi, mu dai mun yi abu don Allah kuma don jama’a, sannan gaskiya kuma tana zuwa daga baya. Sannan duk inda ka ganni, to aiki ne kawai babu wasa, domin ni wajen shakatawa na sojoji (Officers Mess) ba na zuwa, idan kuma akwai wanda zai ce ma ya ganni a wajen koda na minta daya ne, to ina jiran wannan soja ya zo ya fada! Ban taba zuwa ba, bata shan giya ko taba ko wani abu, duk wanda ya ce ma ai soja sai da giya, to ka ce ma sa karya yake, ba sojan asali ba ne na jabu ne! To kila irin wannan ne ya bambanta mu da saura wallahu a’alam.