
Asalin hoton, humairas_varieties
Wata mai harkar dafa girke-girke a Zambia ta shaida wa BBC cewar ba ta ɗaukan jerin abincin da suka fi daɗi na duniya da ake fitarwa da muhimmanci.
Hakan na zuwa ne bayan da shafin Taste Atlas, wanda ya shahara kan tantance abincin da ya fi daɗi a duniya, ya wallafa jerin abinci 95 waɗanda suka fi daɗi a duniya.
Ƙasashen Afirka uku ne kacal girke-girkensu suka samu shiga cikin jerin ƙasashe 50 waɗanda suke da abinci mafi daɗi a duniya.
An fitar da jerin abincin ne bayan da mabiya kafar suka kaɗa ƙuri’a kan irin nau’in abincin da ya fi burge su.
Ƙasashen Afirka da abincinsu ya samu shiga cikin 50 waɗanda suka fi daɗi su ne Algeria, da Afirka ta kudu da kuma Tunisia.
Ƙasashen da aka fi samun abinci mafi daɗi, kamar yadda jerin ya nuna, su ne Italiya, da Girka, da Spain, da Japan, da kuma India.
Sai dai wasu na ganin cewa ba a yi adalci ba a yadda aka jera ƙasashen.
Shahariyyar mai dafa abinci, wadda ta mallaki ɗakin cin abinci na Twaala a Zambia, Lillian Elidah ta ce an fitar da jerin abincin ne ta hanyar jin ra’ayin masu zuwa yawon shaƙatawa.
Ta ce “ƙasashe waɗanda abincinsu suka zo a farko-farko suna daga cikin ƙasashen duniya 10 da suka fi samun baƙuncin masu yawon buɗe ido na ƙasashen Turai, saboda haka dole a zaɓi abincin al’ummar ƙasashen.”
Sai dai ta ce dole ne masu dafa abinci na ƙasar Zambia su ƙara ƙoƙari wurin dawo da ɗanɗanon asali na abincin al’ummar ƙasar, musamman kasancewar ana alaƙanta abincin da talauci.
Ta ƙara da cewa bai dole ne sai baƙi sun ziyarci ƙasar kafin su iya ɗanɗana abincin al’ummarsu ba.
Ta ce za a iya yin haka ta hanyar samar da shirye-shirye na kafafen yaɗa labaru da shafukan sada zumunta domin tallata girke-girke na cikin gida.
Sannan ya kamata hukumomin lura da harkar yawon shaƙatawa na duniya su ƙara himma wajen tallata girke-girken al’ummar Afirka.