Abin da ya sa masu neman mafaka suke rububin zuwa Canada...

Asalin hoton, ELOISE ALANNA/BBC

Bara, kusan bakin haure 40,000 suka shiga kasar Canada ta barauniyar hanya ta wani kauye da ke bayan birnin New York-wanda wannan ne adadi mafi yawa- domin neman mafaka. Da yawansu suna suna zuwa kasar ne da tunanin ta fi tarbar baki sama da Amurka. Amma shin Canada za ta iya jure karbar dimbin bakin nan?

Watarana cikin sanyi, titin Roxham ya kasance tsit. Kwatsam sai ka wata mota ta tunkaro karshen titin ga kuma motsin sahu a dusar kankara.

Kimanin bakin haure 150 ne ake saukewa a wannan wajen a kullum masu burin shiga kasar Canada. Da yawansu sun taso daga can nisan duniya ne har daga Brazil, inda wannan hanyar da ke birnin New York ke kasancewa hanyar isar da su zuwa Canada.

Roxham barauniyar hanya ce. Babu ma’aikatan shige da fice, sai dai ’yan sanda kawai da suke kama masu tsallakawa.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like